Naɗin Ali Ado Dagacin ƙaura Goje abu ne na farin ciki ga al’ummar Gama da ƙaura Goje — Danjummai

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Alhaji Abdullahi Sulaiman, wanda aka fi sani da ɗanjummai, ɗaya daga cikin amintattun abokan sabon Dagacin ƙaura Goje, Alhaji Ali Ado, ya bayyana naɗin da abokinsa ya samu a matsayin wata ni’ima da ta cancanci godiya ga Allah, kasancewar lamari ne mai tsohon tarihi wanda ya gangaro tun daga iyaye da kakanni.

Danjummai ya bayyana haka ne yayin da yake tofa albarkacin bakinsa kan wannan gagarumin ci gaba mai muhimmanci da aka samu a yankin.

A cewarsa, daga cikin waɗanda suka bayar da gagarumar gudummawa wajen tabbatar da wannan naɗi akwai Shugaban ƙaramar Hukumar Nassarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan ɓoye, wanda ya tsaya kai da fata wajen ganin an cimma wannan buri.

“Hon. Ogan ɓoye ɗan uwa ne, ƙani ne, ya yi ƙoƙari matuƙa. Amma wanda ya fara ɓuɓɓuga da wannan tafiya tun asali shi ne tsohon Shugaban ƙaramar Hukumar Nassarawa, Hon. Aranposu. Shi ne ainihin jigon lamarin. Sai Allah ya ba Ogan ɓoye iko ya tabbatar da shi,” inji ɗanjummai.

Ya ce a yanzu suna cikin farin ciki mara misaltuwa, domin Gama da ƙaura Goje abu ɗaya ne, tare suke.

“Gama akwai kwari, akwai tudu, akwai Kanawa, duk abu ɗaya ne, Gama ta haɗu da sama da ƙasa,” ya jaddada.

Da yake magana kan halayen sabon Dagacin, ɗanjummai ya bayyana Alhaji Ali Ado a matsayin mutum mai mu’amala ta gari, mai kula da jama’a, mai riƙe zumunci da abokantaka.

“Abokina ne tun muna ƙananan yara, har yau muna tare, babu abin da ya raba mu har muka kai wannan matsayi,” ya ce.

Ya ƙara da cewa sarautar ba sabuwa ba ce ga Ali Ado, domin mahaifinsa, Alhaji Ado Mai Unguwa, ne, kuma tun yana raye duk wasu ayyukan mulki Ali yake gudanarwa a gefensa.

“Shi mulki a wajensa gado ya yi,” inji shi.

Danjummai ya ce duk da cewa suna murna da naɗin Ali Ado a matsayin Dagacin ƙaura Goje, lamarin ba na murna kaɗai ba ne, domin nauyi ne mai girma wanda Allah zai tambayi mai riƙe da shi a kansa.

“Abin da zai yi shi ne ya yi adalci, ya riƙe gaskiya, ya bai wa kowa haƙƙinsa, mai ƙarfi da mara ƙarfi, idan al’amari ya zo gabansa,” ya shawarce shi.

Alhaji Abdullahi ɗanjummai ya kuma yi kira ga al’ummar da ke ƙarƙashin sabon Dagacin da su yi biyayya ga wanda Allah Ya ba mulki, ko da ɗansu ne, su yi masa biyayya gwargwadon yadda Allah Ya shar’anta, shi kuma ya tabbatar da ba su haƙƙoƙinsu

By ukarofi

Leave a Reply