
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin Gwamnatin Tarayya ra shigar da sabuwar ƙara akan Adeniyi Adeyemi, Darakta-Janar na hukumar da aka yi zargin ta bogi ce, wato Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC).
Lauya ga Antoni Janar na Ƙasa, Rotimi Oyedepo (SAN) ya shaida wa Mai Shari’a Mohammed Umar na Babbar Kotun Tarayya cewa sun riga sun shigar da sabuwar ƙara a Babbar Kotun Abuja. Akan haka ne ya nemi alƙalin ya yi watsi da ƙarar a babbar kotun tarayyar. Ganin cewa lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu (SAN) bai yi inkarin buƙatar ba, Alƙali Umar ya yi watsi da shari’ar.
Alƙalin ya ɗauki wannan mataki ne bayan gwamnatin ta gabatar da wata buƙata da kuma sharaɗin za a mayar da wanda ake zargin zuwa Babbar Kotun Abuja domin fara sabuwar gurfanarwa.
A yayin zaman na ranar Litinin, 12 ga Oktoba, 2026, Rotimi Oyedepo ya gabatar da ƙorafin neman a kawo ƙarshen tuhume-tuhumen a kotun. Ya shaida wa alƙalin cewa Antoni Janar na Ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, ya yi nazari akan takardar ƙarar Adeyemi da wanda Sufeto Janar na Ƙasa ya shigar, inda aka gano akwai waɗansu kurakurai.
Daga dalilan, akwai zargin takardun da Adeyemi ya yi aiki da su a matsayin na bogi wajen gudanar da harkokinsa, wanda Babbar Kotun Abuja ce ya dace a kai wa ƙara a madadin Babbar Kotun Tarayya. Oyedepo, wanda kuma shi ne Daraktan Shari’o’in Al’umma na Tarayya (DPPF), ya ce an shigar da sabuwar ƙara a Babbar Kotun ta FCT kuma za a gurfanar da Adeyemi a matsayin fara sabuwar shari’a.
