
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Cibiyar Aikin Jaridar Binciken Ƙwaf ta Wole Soyinka (WSCIJ) ta naɗa fitaccen ɗan jaridar ɗaukar hoto, Sani Mohammed Maikatanga wanda wakilin Manhaja ne mai ɗaukar hoto, a matsayin ɗaya daga cikin alƙalai a taron bayar da lambar yabo na Wole Soyinka Award for Investigative Reporting (WSAIR) karo na 21.
Wannan taro yana karrama ƙoƙarin ‘yan jarida da suka yi fice ta fuskar haɗa rahotannin da aka zurfafa bincike akansu kafin wallafa su bisa nuna ƙwarewa, ƙirƙira da ƙoƙarin mayar da hankali kan aikin jarida da ya karkata ga maslahar al’umma.
A cewar wata wasiƙa da ke ɗauke da sanya hannun Babban Daraktan WSCIJ, Motunrayo Alaka, kowane mamban tawagar alƙalan zai taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci yayin bayar da kyautar da gano waɗanda suka yi fintinkau a fagen a Nijeriya.
Bayan tantancewa ta farko daga ɓangaren kwamitin tantancewa na cibiyar, za a bai wa alƙalan jaddawalin sunayen waɗanda suka cancanci shiga ɓangarorin waɗanda za a bai wa kyautukan bisa samun maki a ɗaiɗaikunsu. An bayyana cewa, daga acikin waɗanda suka samu shiga jaddawalin da aka bai wa alƙalan ne za a fitar da waɗanda suka yi nasara tare da ba su lambobin karramawa.
Da yake tsokaci kan shiga sahun alƙalan na WSCIJ, Maikatanga ya yi godiya bisa samu kansa acikin acikin jami’an muhimmin taron. Maikatanga, wanda ya taɓa lashe kyautar karramawa ta ƙwararren ɗan jaridar ɗaukar hoton shirye-shirye na musamman, an haife shi ne a ranar 15 ga Agustan 1975 a Unguwar Giginyu da Ƙaramar Hukumar Nassarawan Jihar Kano.
Haka kuma, ya halarci makarantun Giginyu Special Primary School daga 1983 zuwa 1989, Government Secondary School Tarauni daga 1989 zuwa 1991, Federal College of Education Technical Bichi da ke Jihar Kano inda ya yi karatu a Tsangayar Injiniyancin Lantarki.
Kazalika, ya yi aiki a matsayin wakili ko mai ɗaukar hoto na tsawon sama da shekaru 30 a wurare kamar haka; FIM Magazine, Freelance Photojournalist, Leadership Newspaper da Daily Trust, inda ayyukansa da dama BBC Hausa ce ke wallafa su, AP, Reuters, DW da kuma The Guardian.
