Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta kama tsohon gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha, bisa zargin haɗa baki wajen aikata laifi, yin jabun takardu da kuma kwaikwayon wani mutum.
Rahotanni sun ce an kama Okorocha ne a daren ranar Litinin a otal ɗin REIZ Continental da ke Abuja.
Mai magana da yawun rundunar ’yansandan, CSP Aniete Iniedu, ya tabbatar da kama tsohon gwamnan, inda ya ce an sake shi bayan yi masa tambayoyi na tsawon sa’a guda bisa beli.
Ya ƙara da cewa an umarci Okorocha da ya koma hedikwatar rundunar da ke Abuja a ranar Talata domin ci gaba da yi masa tambayoyi yayin da bincike kan zargin ke gudana.
Rahoton ya ce kamen ya biyo bayan rashin amsa gayyatar da ’yansanda suka yi masa a baya. An fara gayyatarsa ne a ranar 2 ga Satumba, amma aka sauya ranar zuwa 8 ga Satumba bisa buƙatar lauyoyinsa, sai dai rahoton ya ce bai halarci ganawar ba.
