Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da kashi 4.2 cikin 100 a shekarar 2026, amma ya yi gargaɗin cewa hauhawar farashin kayayyakin masarufi na iya sake jefa miliyoyin ’yan ƙasar cikin matsanancin talauci da ƙarancin abinci.
IMF ya bayyana hakan ne a wani rahoto da ya gabatar yayin taron haɗin gwiwa tsakaninsa da Bankin Duniya, wanda ke gudana a birnin Bangkok na ƙasar Thailand. Taron na tattauna batutuwan da suka shafi juriya a lokacin matsin tattalin arziki da kuma hanyoyin magance matsalolin da ke tasowa cikin gaggawa.
A cewar rahoton, duk da cewa tattalin arzikin Nijeriya na nuna alamun bunƙasa kuma ba a sa ran zai fuskanci wata babbar matsala nan kusa, har yanzu akwai yiwuwar miliyoyin ’yan ƙasar su ci gaba da shiga cikin mawuyacin hali na talauci.
Asusun ya danganta wannan barazana da hauhawar farashin kayayyakin yau da kullum, wanda ke ƙara wa al’umma wahalar biyan buƙatun rayuwa, musamman abinci da sauran muhimman kayayyaki.
Rahoton ya nuna cewa manyan sauye-sauyen manufofin tattalin arziki da gwamnatin Nijeriya ta aiwatar sun taimaka wajen rage barazanar faɗawar ƙasar cikin matsanancin rikicin tattalin arziki. Sai dai, waɗannan matakai sun kuma ƙara matsin rayuwa ga miliyoyin ’yan ƙasar sakamakon tsadar kayayyaki da sauran matsalolin tattalin arziki.
Daga cikin sauye-sauyen da IMF ya yi tsokaci a kansu akwai gyare-gyaren da aka yi a kasuwar musayar kuɗaɗen ƙetare da kuma cire tallafin man fetur. A cewar rahoton, waɗannan matakai sun taimaka wajen inganta wasu sassan tattalin arzikin ƙasar, amma sun kuma jefa jama’a cikin ƙarin matsin kuɗi.
IMF ya kuma yi hasashen cewa tattalin arzikin Nijeriya zai bunƙasa da kashi 4.3 cikin 100 a shekarar 2027.
A halin da ake ciki, ana sa ran tattalin arzikin ƙasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara zai bunƙasa da kashi 4.5 cikin 100 zuwa ƙarshen shekarar 2026.
Hasashen IMF ya sake jaddada bambancin da ke tsakanin bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da ingantuwar rayuwar jama’a, domin ƙaruwa ko bunƙasar tattalin arziki ba lallai ne ta haifar da raguwar talauci nan take ba idan farashin kayayyaki da sauran buƙatun yau da kullum na ci gaba da hauhawa.
