Raɗɗa ya nemi tallafin TETFund ga manyan makarantu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira da a cigaba da tallafawa manyan makarantu da ke Jihar Katsina ta hannun Asusun Tallafawa Ilimin Manyan Makarantu (TETFund), inda ya yaba da gagarumar gudummawar da asusun ke bayarwa wajen bunƙasa harkokin ilimi, musamman tallafin da yake bai wa jami’ar kimiyyar lafiya da magunguna ta tarayya da ke Funtua.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a yayin da yake gabatar da saƙon fatan alheri a taron tattaunawa da jama’a na ƙasa karo na biyu da TETFund ta shirya a Abuja.

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, kuma Shugaban kwamitin amintattu na TETFund, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ne ya jagoranci taron, wanda aka shirya domin bayyana nasarorin da asusun ya samu, inganta riƙon amana da kuma ƙarfafa hulɗa da jama’a kan yadda ake samar da kuɗaɗen gudanar da manyan makarantu.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa halartar taron nasa ya samo asali ne daga girmamawar da yake yi wa jagorancin Masari, da kuma yadda gwamnatinsa ke yaba wa ci gaba da tallafin da TETFund ke bayarwa wajen bunƙasa ilimi a Jihar Katsina.

Gwamnan ya ce: “Na zo nan ne saboda manyan dalilai guda biyu. Na farko, wannan taro ne da tsohon shugabana, tsohon Gwamnan Jihar Katsina kuma shugaban kwamitin amintattu na TETFund, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ke jagoranta. Ina matuƙar girmama jagorancinsa da gudummawar da ya bayar.

“Dalili na na biyu shi ne domin bayyana matuƙar godiyarmu bisa gagarumin tallafin da TETFund ke ci gaba da bai wa manyan makarantunmu.”

Gwamnan ya bayyana cewa tallafin TETFund ya zama muhimmin ginshiƙi wajen ƙarfafa gine-ginen makarantu, inganta muhallin koyarwa da karatu, da kuma bunƙasa ƙarfin manyan makarantu wajen samar da ingantaccen ilimi.

Ya ƙara da cewa: “Idan mutum ya yi tunanin irin ƙalubalen da manyan makarantunmu za su fuskanta ba tare da waɗannan muhimman tallafe-tallafe ba, zai fahimci girman amfaninsu. Muna matuƙar godiya da tallafin da TETFund ke cigaba da baiwa makarantunmu, domin waɗannan zuba jari suna da muhimmanci ga ci gaba da bunƙasar ilimin manyan makarantu.”

Gwamna Raɗɗa ya kuma bayyana godiyarsa ta musamman ga TETFund bisa tallafin da take bai wa Jami’ar Kimiyyar Lafiya da Magunguna ta Tarayya da ke Funtua, inda ya bayyana jami’ar a matsayin wata muhimmiyar kafa da ta ƙara wa harkokin ilimin manyan makarantu a Jihar Katsina da ma yankin Arewa maso Yamma ƙarfi.

Gwamnan ya jaddada cewa ci gaba da zuba jari a ilimin manyan makarantu yana da matuƙar muhimmanci wajen faɗaɗa damar samun ilimi ga matasa, ƙarfafa cibiyoyin ilimi da samar da ƙwararrun ma’aikata waɗanda za su taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Najeriya, ƙirƙire-ƙirƙire a fannin kimiyya da kuma ci gaban fasaha.

Haka kuma, ya yaba wa Shugaban kwamitin amintattu na TETFund, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, bisa jagorancinsa da kuma ci gaba da hulɗarsa da masu ruwa da tsaki waɗanda suka himmatu wajen bunƙasa ilimi a faɗin ƙasar nan.

By ukarofi

Leave a Reply