Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Farko waɗanda a ‘yan watannin nan ke yunƙurin ruruta fitinar ƙabilanci a Arewa da ke da taken Zallawa sun ɗauka za a ji tsoronsu don kar su ce mai haska su Bafulatani ne ko ya na kare ‘yan ta’adda. Idan zaman Zallawa wasu mutane ne daga ƙananan ƙabilu bai zama damuwa ba, mai ya sa zama Bafulatani ko Bahaushe zai zama matsala?
Ba tun yau ba na haska mu ku karatun cewa ko ma akwai masu iƙirarin su Hausawa ne a cikin Zallawa, to sun kulle kiyayya mai tsanani ga mafi rinjayen Hausawa waɗanda Musulmi ne inda su ka yi kuskuren ɗaukar Shehu Danfodiyo ne ya tilasta Hausawa da sauran jama’a tsayawa kan Musulunci maimakon bin addinin gargajiya. Wannan ya sa Zallawa maida aibatawa da zagin Mujaddadi kan gaba a farafagandarsu.
An wayi gari an ga wasu ƙabilu ban da ma AIFOB da su ke aikin zallanci da musamman su ka haɗa da wasu masu kafa tarko su tare hanya su kashe matafiya inda in an zo bincike ko naman gawa, sai matansu tsoffi su yi caaa wai za su yi tsirara matuƙar ba a janye binciken ba. Akwai kuma wasunsu ma da irin na su samfurin zallancin ya na da alaƙa da zuga daga waɗanda ba sa ƙaunar zaman lafiya a Lardin Arewa.
A taƙaice in har irin waɗannan mutanen da sauran Midibelawa na kundunbala a zalllanci don yaƙi da musulunci da sunan adawa da Shehu Mujaddadi, me laifin mutum in ya zama Bafulatani ko Bahaushe Musulmi? In ba ƙungurmin mai son tada zaune tsaye ba, wa ke alƙanta mugunta da ƙabila? ɗaya daga mutanen da a ke magana na nan a iya jihar Kaduna kuma kowa ya san yanayinsu balle a je ga zaman doya da manja tsakanin ƙabilun jihar Filato da mata tsoffi kan nemi yin tsirara wai kar a binciki ’ya’yansu da su ka yi kisan gilla ta hanyar tare matafiya da ba su ji ba ba su gani ba.. Ba ma wanda ke kushe Igbo in ba batun AIFOB da ke zama haramtacciyar ƙungiya don mallakar rundunar ESN mai ta’addanci ba.
Kowa ya haska Zallawa, za su yi wuf su ce Bafulatani ne, su ya su ma kan jefi juna da zama Fulani don neman tasiri da zama jagora kan kwangilar nan da ta rikiɗe neman kuɗi a hannun ‘yan siyasa marar sa farin jini da masu son bin ɓarauniyar hanya don hayewa madafun iko.
Da zarar sanannen mutum ya fito fili ya ja hankali kan illar Zallawa, sai boyayyun mutane su yi caaa su na ƙunduma zagi da zayyana shi da Bafulatani. Mun ma rufe mu su baki ruff da ambatar “Agwai” don an gano kabilun Midibelawa ke amfani da kalmar don su ba sa so a gano ɓatar da sawu da su ke yi.
Shin waye mai makirci tsakanin wanda zai fito fili ya haska abun da ya ke gani makirci ne, da taron ɓoyayyu ba suna ba adireshi da kan maida martani?
A nan zan yi amfani da dama wajen kira ga reshen arewa na ƙungiyar Kiristoci ta Nijeriya “CAN” ya tsawatawa zallawa don zama rigakafi
Haƙiƙa duk ƙungiyoyin mabiya addinin Kirista a Nijeriya kama daga ‘yan ɗarikar katolika, Cocin Pentacostal, Aladura Cherubim da Seraphim, Redeem, ECWA da sauransu na bin umurnin babbar laimar CAN. Ina amfani da wannan dama wajen kira ga reshen ƙungiyar na Arewa ya ja hankalin wasu mabiya da ke neman ruruta fitinar ƙabilanci. Gaskiya har yau ban ga sharhin AREWA/CAN kan nada sarkin mabiya Hausawa na Kano ba, hakanan ban ga bayani kan nesanta kai daga Aleɗ Birbir ba ko wasu kalamai na Rabaran Dochomo da ke neman aibata Allah maɗaukakin sarki.
Kwanaki na kawo ƙungiyoyi da dama na Hausa/Kiristan da ke daukar matsaya da ba ta kan tafarkin zaman lafiya. Wallahi na ja hankalin daya daga abokai na da ya rike babban muƙami a helkwatar CAN a Abuja kan wannan lamari. Na sha shiga helkwatar don tattaunawa kan lamura masu muhimmanci. Abokin nawa ya nuna aniyar yin abun da ya dace kan kashe bakin wutar gungumen da a ke ta iza ma sa wuta da zuga-zugi don in ya kama bau sai duk dajin ya ɗauka. Idan an bar matakin ya kai har nan, to gaskiya motocin kashe gobara ba za su yi tasiri ba sai wajen sharar gawayi da kawar da toka. Allah ya sauwaƙe ya kare Arewa da dukkan al’ummar Arewa da tarayyar Nijeriya.
Wasu daga mabiya ‘yan ƙabilar Berom daga Filato na furta kalamai ba tare da damuwa da ko ma meye zai zo ba. Su kan bukaci aiki tare da masu iƙirarin Hausa zalla don tayar da fitina a Arewacin Nijeriya. Kowa ya san kalaman Zallawa na neman zuga musulmi su yi ta ɗauki ba daɗi a doron ƙabilanci, kowa na ganin yadda Zallawa ke zagin Shehu Mujaddadi da manyan malaman Musulunci, kowa na ganin barazar da Zallawa ke yi wa manyan sarakunan Arewa da jifar su da miyagun kalamai na izgilanci da kazanta. Gaskiyar magana aiki ne mai muhimmanci shugabannin mabiya su yi amfani da ikilisiya wajen jan kunnen wadanda su ka bijire su dawo kan hanya. Wallahi duk fitinar da za ta shafi Arewa kusan duk ƙasar za ta iya ɗauka kuma zai ma yiwu masu rura wutar su za su fara kamawa da wuta.
Allah ya sani ba a so na ko daɗin abun da na ke rubutawa na ke ji ba, a’a abun da na hango ne a ‘yan shekarun da na yi ina aiki da hulɗa da jama’a. Haƙiƙa ko mutum ya na so ko ba ya so, muguwar ɗabi’a ba ta da ƙabila kuma ba ta da addini amma shaidanu ka iya fakewa da wata manufa don kunna fitina da zummar cimma burin ‘yan aware da sauran mahassada masu baƙar zuciya.
Duk yadda zallawa ke ƙunduma ashar amma su na ɓoye ruff a wayar salula kuma
da ka yi magana sai su yi ta wurgo hotunan ‘yan ta’adda don shashantar da kalubalen. Ba mai kiɗimewa fa haka kurum a tsakanin jama’a kuma wautar mutane ma ba ta kai mizanin wasu su ɓoye kansu su buɗe shafuka barkatai na shirme su na iƙirarin wai Hausawa su ke karewa! Da a ka yi me ko a kan me? Shin mai ya sa mai kare wani har da naɗa kansa wai dan gwagwarmaya zai buya ba hoto ba sunan gaskiya ga karyar mannewa musulunci don samun damar rutsawa da waɗanda ba su yi aune ba.
Ko taron da Zallawa su ka yi kwanaki sai wasu ‘yan tsirarun nan kawai su ka iya ambatar sunansu amma ba su bi layi-layi su na gabatar da kansu ba. Da na kara dubawa ma duk mahalarta masu sauraron ‘yan yara ne kanana da ba su san inda duniya ta dosa ba da hakan ke nuna an yaudare su ne. Kawai an nuna mutane ne a zaune shiru sai in bukatar tafi ta samu. Kazalika ni ban ga an nuna wanda ya daga hannu ya yi tambaya ba. Duk taro na buƙatar gabatar da ajanda da kuma mai babbar magana da wanda zai yi sharhi.
Akasari ka ga Bazalle ya bayyana to ya fito a shafinsa na gaskiya ne daga doron kabilarsa ko iyayen giji AIFOB. Idan ka ga wani malamin addini ya mara mu su baya za ka ga malamin bushara ne da ba mamaki ko yawace-yawace a ƙauyuka ko kuma mai ikirarin Musulunci amma ko gyaran fuska ba ya yi don dama kura ce da fatar akuya ba annurin Islama ko kwayar zarra a fuskarsa kamar ya na kwana a rumfar kasuwar kauye. Akwai wani ma mai zazzare idanu daga cikin tabarau wai gugar zana ya ke yi wa manyan malaman Musulunci.
ME ZALLAWA KE ɓOYEWA YA SA SU KE ɓOYE RUFF?
Ga dalilai 4:
1. Akasarinsu ba musulmi ba ne kuma kwangialarsu ita ce ta hada Musulmi faɗa da juna don haka in sun fito a mutum ba za a amince da su ba. Don haka buyan ne kawai logar bagaye ko batar da sawu.
2. Wasunsu sanannun mutane ne a jami’o’i da su ka ci gajiyar Sir. Ahmadu Bello amma bijirewa ta yi wa zuciyarsu kanta don haka sai su bude shafukan bogi don samun damar amayar da gubarsu. A gaskiya ba sa lura da sakamakon da zai iya biyo bayan kalamansu ba.
3.Tun da bila-adadin ba Hausawa ba ne don haka fitowarsu fili da ƙirƙiro karyar kare Hausawa ba za ta kai labari ba don mai ɗaki shi ya san inda ya ke yi ma sa yoyo. Sai wanda ya tashi a tsakanin Hausawa ne akasari ya kan iya magana tar-tar ba tare da jefa gwarancin harshe ba.
4. Akwai waɗanda ke fargabar kar hukuma ta cafke su don sharrin da su ke antayawa a soshiyal midiya, sai su ka ɗauka in sun kasance a rufe ruff za su ci karensu ba babbaka. Wannan ma ba dabara ba ce don matukar mutum ya hau yanar gizo za a iya gano shi da fasahar na’ura.
KAMMALAWA
Mun gode wa Allah da yanzu na ga Zallawa, su ya su ke kiɗansu su yi rawansu amma Hausawa da al’ummar Arewa sun gane makircin da a ke ƙullawa.
