An kammala makon ɗalibai karo na farko a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

An kammala bikin makon ɗalibai a karo na farko ƙarƙashin ofishin mai taimaka ma gwamnan Jihar Katsina akan harkokin ɗalibai, Hon. Muhammad Nuhu Nagaske ya shirya.

Taron da aka ɗauki tsawon kwanaki biyar ana gudanarwa sun haɗa da gasannin ilimi, wasanni da al’adu, tsakanin ɗaliban makarantun daban-daban dake ɗauke da ɗaliban jihar Katsina gami da miƙa kyaututtuka gare su.

Da yake gabatar da jawabin maraba, Hon. Muhammad Nuhu Nagaske ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da aka samu wajen gudanar da makon ɗaliban na tsawon kwanaki huɗu.

Ya ce bikin ya samar da dama ga ɗaliban Jihar Katsina wajen nuna hazaƙarsu a ilimi, wasanni da al’adu, tare da haɗa kan ɗalibai daga makarantu daban-daban.

Nagaske ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, bisa kulawa da damuwar da yake nunawa kan harkokin ɗalibai, Inda yace goyon bayan gwamnan na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen ganin an samu nasarar wannan shiri.

A jawabin shugaban kwamitin tsare tsare na taron Dr. Bashir Usman Ruwangodiya ya yi yabo da jinjina ga gwamnan jihar Katsina bisa wannan abu da yazo da na alkhairi ga ɗaliban jihar Katsina tare da kira gare sa da wannan shiri ya ɗore domin ɗaliban jihar Katsina.

Da yake gabatar da jawabin sa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD ya jaddada muhimmancin ilimi wajen gina makomar matasa da ci gaban jihar.

Gwamnan ya yaba wa masu shirya taron, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da bai wa ilimi da harkokin ɗalibai muhimmanci. Ya kuma buƙaci ɗalibai da su mayar da hankali kan karatu, su bunƙasa basirarsu, tare da amfani da iliminsu wajen taimakon al’umma.

A yayin taron, an bada kyaututtuka ga ɗalibai da makarantun da suka yi nasara a gasannin da aka gudanar cikin kwanaki huɗu.

Kyaututtukan sun haɗa da makudan kuɗaɗe da sauran kyautuka, domin ƙara zaburar da dalibai wajen ƙoƙari a ɓangarorin ilimi, wasanni da al’adu.

Mutane da dama ne suka gabatar da jawabai a wurin taron wanda suka haɗa Dr. Mustapha Shehu, Hon. Lawal Rufai Safana, Dr. Babangida Ruma da sauran su.

Taron da ya gudana a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua UMYU ya sami halartar sauran manyan makarantu dake faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply