
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zargi jam’iyyun adawa da samar da yunwa da talauci acikin al’umma da ake sukar gwamnatinsa akansu a yau, inda ya ce gwamnatin tana aiki tuƙuru don ganin ta shawo kan matsalolin tattalin arziƙi da al’umma ke fama da ita.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Asabar yayin taron buɗe gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, inda ya nemi al’umma da su sake zaɓar sa a karo na biyu domin cigaba da samun nasarori da farfaɗowar harkar tattali. “Na ji abokan adawata suna magana akan yunwa da talauci. Su waye suka samar da shi? Su ne. Mu na ƙoƙarin kawo ƙarshensa,” inji Shugaban ƙasar.
Ya kirayi ‘yan Nijeriya da su goyi bayan tsare-tsaren gwamnatinsa, inda ya ce tana aiki tuƙuru wajen biyan ma’aikata albashinsu akan kari da samar wa ‘yan ƙasa damarmaki. Ya kuma yi kira ga masu zaɓe da su tabbatar da sun tanadi katin zaɓensu (PVC) tare da shiga zaɓen shugaban ƙasar da ke tafe a 2027.
A cewarsa, gwamnatin ta samar wa ‘yan Nijeriya nasarori, ci-gaba, farfaɗowa da damarmaki, yayin da ya zargi ‘yan adawa da dogara da ƙiyaye akan gabatar sahihan mafita ga ababen da suke iƙirarin an gaza akansu. Ya kuma roƙi magoya baya da su zaɓi APC a dukkan matakai tun daga shugaban ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisar dokokin ƙasa da ‘yan majalisar dokokin jihohi.
Kazalika, Shugaban Nijeriyar ya jinjina wa gwamnonin APC kan abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarin samar da ci-gaba a jihohinsu, yana mai bayar da misali da kiyaye biyan albashin ma’aikata akan lokaci.
A ƙarshe, ya buƙaci magoya baya da su kasance masu lura kan labaran bogi masu ruɗarwa da kar yaɗawa musamman a wannan zamani da yawaitar amfani da fasahar AI wajen samar da bayanan ƙarya tare da kira ga su cigaba da nuna wa gwamnatinsa goyon, yana mai alƙawarin samar da gobe mai kyau a ƙarƙashin mulkinsa.

