Ku fita batun farfagandar ‘yan mediya, ‘yan Nijeriya na son Tinubu – Ministan Labarai

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan ‘Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris Malagi, ya yi jinjina ga taron buɗe yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2027 da jam’iyyar APC ta jagoranta, wanda kwamitin yaƙin neman zaɓenta (APC-PCC) ya shirya da nufin neman a sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu a karo na biyu na wa’adin mulki.

Mohammed Idris ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin gangamin buɗe yaƙin na APC a Jihar Kaduna, inda ya bayyana ƙwarin-gwiwa kan shaharar Tinubu da goyon bayan al’umma ga ajandar gyare-gyaren gwamnatinsa. Ya bayyana dandazon jama’ar da suka halarci taron a matsayin ishara kan cewa Tinubu ya samu karɓuwa acikin ‘yan Nijeriya, musamman magoya bayan da suka amince da tsare-tsarensa.

Ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su riƙa kawar da kai kan rahotannin Soshiyal Mediya da sukar ‘yan adawa, inda ya ce cikar farin dangon jama’a a gangamin ya nuna gagarumin goyon baya ga Tinubu. “Mun jima muna faɗar wannan: ku manta da dukkan wani labari na soshiyal mediya, ku manta da dukkan wani abin da ‘yan adawa suke faɗa. ‘Yan Nijeriya suna ƙaunar Asiwaju,” inji Ministan.

Ya ƙara da cewa, Jihar Kaduna ce ya dace a buɗe gangamin yaƙin neman zaɓen kasancewarta mai dogon tarihi a matsayinta na tsohuwar babban birnin Arewacin Nijeriya.

A cewarsa, ganin magoya baya daga ɓangarorin siyasa mabambanta ya nuna yadda al’umma suka amince su haɗe wajen mara wa Tinubu da ajandar gyare-gyaren gwamnatinsa baya, yana mai cewa ‘yan Nijeriya suna ƙara fahimtar amfanin tsare-tsaren gwamnatinsa da ƙoƙarin farfaɗowa a harkar tattali.

Ministan ya ce ƙasar tana fama da ƙalubale da dama amma kuma gyare-gyaren gwamnatin za su bunƙasa halin tattalin arziƙi, inda ya kuma bayyana ƙwarin-gwiwar cewa ‘yan ƙasa za su sake zaɓar Tinubu a karo na biyu a zaɓen 2027.

By Babaji

Leave a Reply