Cacar baki ta kaure tsakanin FAAC da NNPC kan ɗanyen fetur ga matatar Dangote a Yuli

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMAD

Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) ya bayyana cewa Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC) ya fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje a watan Yulin 2026, amma bai yi wata cinikayya ta ɗanyen mai a cikin Nijeriya ba a wannan lokacin. Sai dai NNPC ya ce ya samar da ganga miliyan 8.16 na ɗanyen mai ga Matatar Man Fetur ta Dangote a cikin watan.

Wannan saɓani ya fito ne daga rahoton ƙaramin kwamitin fasaha na FAAC mai kwanan wata 14 ga Oktoba, wanda ya bayyana bayanan cinikin ɗanyen mai da iskar gas na NNPC, ƙimar kayayyakin da aka sayar da kuma kuɗaɗen da kamfanin ya karɓa a watan da ake magana a kai.

A cewar rahoton, Shugaban NNPC, Bayo Ojulari, ya bayar da bayanin cewa an fitar da ganga miliyan 1.27 na ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje a watan Yulin 2026, kan kuɗin da ya kai naira biliyan 149.6, kwatankwacin dala miliyan 112.38. Sai dai rahoton ya ambato wakilin NNPC yana cewa ba a sayar da ɗanyen mai ga masu amfani da shi a cikin gida ba a watan Yulin.

Game da cinikin ɗanyen mai da aka fitar zuwa ƙasashen waje, kwamitin ya ce NNPC ta karɓi naira biliyan 40.04, kwatankwacin dala miliyan 30.06, a watan da ake nazari. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu ƙarin kuɗaɗen shiga daga wasu mu’amaloli da suka shafi ɗanyen mai, waɗanda suka kai naira miliyan 12.28, kwatankwacin dala 9,222.

Dangane da cinikin iskar gas kuwa, wakilin NNPC ya bayyana cewa an sayar da tan miliyan 6.57 na iskar gas zuwa ƙasashen waje a watan Yulin, kan kuɗin da ya kai naira biliyan 19.44, kwatankwacin dala miliyan 14.59. Rahoton ya ƙara da cewa kamfanin ya karɓi naira biliyan 7.11, wato dala miliyan 5.34, daga wannan ciniki a cikin watan. Haka kuma, an samu naira miliyan 24.13, kwatankwacin dala 18,116, daga wasu mu’amaloli da suka shafi iskar gas.

Shugaban NNPC ya kuma bayar da rahoton cewa an sayar da tan miliyan 1.25 na iskar gas a cikin gida a watan Yulin, kan kuɗin da ya kai naira biliyan 2.23. Sai dai rahoton ya nuna cewa ba a rubuta wani kuɗin da aka karɓa daga wannan ciniki a cikin watan ba. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, NNPC ba ta mayar da martani ga tambayoyin da aka aika mata kan bambancin da ke tsakanin ƙimar kayayyakin da aka ce an sayar da kuma kuɗaɗen da aka tabbatar an karɓa ba.

Da yake magana kan samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da kuma fitar da shi zuwa ƙasashen waje, mai magana da yawun NNPC, Andy Odeh, ya ce kamfanin na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da wadatar makamashi a Nijeriya da kuma bin tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA).

Odeh ya bayyana cewa NNPC na ci gaba da samar da ɗanyen mai ga matatun da ke cikin ƙasar, ciki har da Matatar Man Fetur ta Dangote. Ya ce, NNPC ta samar da ganga 8,166,170 na ɗanyen mai ga matatar Dangote a watan Yulin 2026. Wannan bayani ya saɓa da abin da rahoton FAAC ya bayyana na cewa ba a yi cinikin ɗanyen mai a cikin gida ba a wannan watan.

Odeh ya ce NNPC Limited ta fara yarjejeniyar saye da sayarwa da Matatar Dangote tun shekarar 2023, kuma yarjejeniyar shekaru biyu da ake aiki da ita a yanzu, wadda ta fara aiki a watan Agustan 2025, tana nan daram kuma za a sabunta ta idan wa’adinta ya ƙare.

By ukarofi

Leave a Reply