Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya bayyana cewa, Majalisar Masarautar Sakkwato tana ƙoƙarin kafa sabon bankin Musulunci mai suna Caliphate Islamic Microfinance Bank, domin yaƙi da talauci, samar da ayyukan yi da kuma bunƙasa hanyoyin dogaro da kai a Nijeriya da ƙasashen Yammacin Afirka.
Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Lahadi a Sakkwato, yayin buɗe wani horo na kwanaki uku da aka shirya domin ƙarfafa ƙwarewar masu ruwa da tsaki kan tsarin Baitul Mal wat Tamweel (BMT), wanda ya haɗa kula da walwalar al’umma da samar da tallafin kuɗi don bunƙasa tattalin arziki.
Bankin Raya ƙasashen Musulunci (IsDB) ne ya shirya horon tare da haɗin gwiwar Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Sakkwato. Sarkin, wanda Hakimin Kilgore, Alhaji Jabbi Kilgore, ya wakilta a wajen taron, ya ce bankin da ake shirin kafawa zai bai wa ƙananan ’yan kasuwa damar samun kuɗaɗen gudanar da kasuwancinsu bisa ƙa’idojin Musulunci, domin faɗaɗa harkokinsu, samar da ayyukan yi da inganta rayuwarsu.
Ya bayyana cewa aikin kafa bankin ya kai wani mataki na ci gaba, inda masu zuba jari, ciki har da waɗanda ke wajen Nijeriya, suka nuna sha’awar haɗa kai wajen ganin an cimma wannan buri. “Ana son kafa bankin da zai zama abin koyi, ba ga Nijeriya kaɗai ba, har ma da sauran ƙasashen yankin Yammacin Afirka,” inji shi.
Sarkin Musulmi ya bayyana haɗin gwiwar Bankin Raya ƙasashen Musulunci da Hukumar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato a matsayin wani muhimmin mataki na rage talauci, ta hanyar inganta tattara zakka, tafiyar da ita yadda ya kamata da kuma amfani da kuɗaɗen agaji wajen ayyukan da za su amfani al’umma na dogon lokaci.
Ya buƙaci mahalarta horon da masu gabatar da jawabai da su tabbatar da cewa ilimin da aka samu ya haifar da matakai na zahiri da za su inganta rayuwar masu rauni a cikin al’umma, tare da ƙarfafa ƙoƙarin yaƙi da talauci.
Da yake magana a wajen taron, Shugaban ƙungiyar Zakka da Wakafi ta Jihar Sakkwato, Malam Lawal Maidoki, ya yi kira da a sauya salon dogaro da zakka da sauran tallafin agaji kawai, zuwa samar da ayyukan dogaro da kai da za su taimaka wa waɗanda ke amfana da tallafin su tsaya da ƙafafunsu.
Maidoki ya ce tsarin BMT yana haɗa tallafin jinƙai da bunƙasa tattalin arziki, ta hanyar ba wa masu rauni agajin gaggawa, sannan ya taimaka musu wajen samun kuɗaɗe da ƙwarewar da za su iya amfani da su wajen gina rayuwa mai ɗorewa. Ya bayyana cewa, duk da muhimmancin zakka da sauran gudunmawar agaji wajen rage wa iyalai marasa galihu wahala, ya kamata a haɗa irin wannan tallafi da damar kafa sana’o’i da kasuwanci, samun kuɗin shiga da kuma fita daga ƙangin talauci a hankali.
Maidoki ya ce, a wasu al’ummomi, zakka da sauran kuɗaɗen agaji suna taimaka wa mabukata wajen biyan buƙatun yau da kullum, amma tallafin kaɗai ba ya samar musu da tabbatacciyar hanyar fita daga matsin rayuwa zuwa dogaro da kai na dindindin. Ya ƙara da cewa, wasu tsare-tsaren ƙananan rance na yau da kullum ba sa dacewa da wasu mabuƙata, musamman waɗanda ba za su iya cika sharuddan samun rancen ba ko kuma suke son samun kuɗaɗen da suka dace da koyarwar Musulunci.
A cewarsa, tsarin BMT yana tattarawa da rarraba kuɗaɗen jinƙai, ciki har da zakka, sadaka da waƙafi, ga waɗanda suka cancanci amfana da su. Haka kuma, yana tallafa wa ayyukan samar da kuɗin shiga ta hanyar hidimomin kuɗi da suka dace da Shari’ar Musulunci, tare da ba da taimakon bunƙasa kasuwanci. Ya ce wannan tsari zai iya ƙara inganta yaƙi da talauci ta hanyar haɗa kariyar walwalar al’umma da ƙarfafa tattalin arzikin mutane, har masu rauni su samu damar dogaro da kansu ta fuskar kuɗi.
Tun da farko, ɗaya daga cikin masu gabatar da jawabai, Saat Suharto, wani mai fafutukar jinƙai daga Indonesiya kuma ƙwararre kan tattalin arziki da harkokin kuɗi bisa tsarin Musulunci, ya ce an shirya horon ne domin ƙarfafa ƙwarewar masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da tsarin BMT cikin adalci, riƙon amana da kuma la’akari da yanayin al’ummomin da za su amfana.
Suharto ya bayyana cewa shirin zai taimaka wa matalauta da sauran masu rauni wajen gina hanyoyin samun abin dogaro da kai na dogon lokaci, har su kai matsayin da za su iya samun ƙarfin kuɗi su riƙa bayar da zakka da kansu a nan gaba. Ya ƙara da cewa, horon ya jaddada buƙatar inganta yadda ake tafiyar da harkokin zakka da wakafi, ƙara wa ma’aikata ƙwarewa, sauƙaƙa hanyoyin gudanar da aiki da kuma amfani da fasaha domin ƙara gaskiya, riƙon amana da ingancin ayyuka.
