Masana binciken kayan tarihi a Turkiyya sun gano wasu tarkacen kayan da ake zargin sun fito daga wani tsohon jirgin ruwa da ya nutse a teku kusan shekaru 4,700 da suka gabata.
Idan ƙarin bincike ya tabbatar da hasashen masana, wannan bincike na iya zama ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da suka taimaka wajen fahimtar tarihin zirga-zirgar jiragen ruwa da kasuwancin teku a zamanin da.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne cewa, duk da tsawon lokacin da aka yi tun bayan nutsewar jirgin, wasu kayayyakin da ake zargin yana cauke da su sun ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin ruwa. Daga cikin abubuwan da aka gano akwai wasu tulunan yumɓu da ake kira amphorae, waɗanda aka saba amfani da su a zamanin da wajen adana da jigilar kayayyaki.
An gano waɗannan kayayyaki a ƙarƙashin ruwa mai zurfin kusan ƙafa 100, a wani yanki kusa da tsibirin Kekova da ke gabar tekun Turkiyya.
Masu binciken sun ce tulunan na iya taimakawa wajen gano irin kayayyakin da ake jigilarwa a lokacin, inda aka samo su, da kuma yadda al’ummomin zamanin da suka yi amfani da teku wajen kasuwanci da hulɗa da juna.
Tsibirin Kekova yana cikin yankin gabar tekun Turkiyya da ya shahara wajen abubuwan tarihi da ke ƙarƙashin ruwa. Yankin yana da tarihin tsoffin matsugunai da gine-gine, kuma masu bincike sun daɗe suna gudanar da ayyukan gano kayayyakin tarihi a yankunan da ke kewaye da shi.
A wannan karon, abin da ya ja hankalin masana shi ne tulunan yumbu da aka gano a wani wuri mai zurfi a cikin teku. An yi zargin cewa waɗannan kayayyaki na iya kasancewa ragowar kayan da wani jirgin ruwa ya ɗauka kafin ya nutse.
A irin waɗannan bincike, masana ba sa dogara da siffar abu kawai wajen tantance shekarunsa. Suna amfani da bayanai daban-daban, ciki har da salon da aka ƙera shi, irin kayan da aka yi amfani da su, wurin da aka samo shi da kuma kwatanta shi da wasu kayan tarihi da aka riga aka tantance shekarunsu.
Saboda haka, gano tulunan yumbu masu tsohon salo na iya zama muhimmin mataki wajen gano tarihin jirgin, amma ana buƙatar ƙarin nazari kafin a tabbatar da cikakken labarin abin da ya faru.
Rahotannin binciken sun nuna cewa ana ganin kayayyakin na iya kasancewa cikin tsofaffin abubuwan da aka taɓa samu da ke da alaƙa da nutsewar jirgin ruwa. Sai dai, yayin da ake ci gaba da bincike, yana da muhimmanci a bambanta tsakanin shekarun kayan da aka gano da kuma shekarun da jirgin ya nutse
