Zaɓen neman ‘yancin kai: Alberta ta zaɓi ci gaba da zama ƙarƙashin Kanada

Spread the love

Al’ummar lardin Alberta da ke Kanada sun kada ƙuri’ar nuna goyon bayansu ga ci gaba da kasancewa cikin ƙasar, maimakon ɗaukar matakin fara hanyar raba lardin da Kanada domin ya zama ƙasa mai cin gashin kanta.

Sakamakon zaɓen raba gardama da aka gudanar ya nuna cewa mafi yawan waɗanda suka kada ƙuri’a sun goyi bayan ci gaba da kasancewa cikin Kanada. Wannan shi ne karon farko da aka gudanar da irin wannan zaɓe a lardin kan batun rabuwa da ƙasar.

Rahoton Reuters ya nuna cewa bayan kashi 33 cikin 100 na ƙuri’un da aka ƙirga, kusan kashi 76 cikin 100 sun goyi bayan ci gaba da kasancewa cikin Kanada, yayin da kusan kashi 23 cikin 100 suka goyi bayan a ɗauki matakin gudanar da zaɓen raba gardama mai ɗaurewa kan samun ‘yancin kai.

Sai dai zaɓen da aka gudanar ba shi da ikon tilasta wa hukumomi ɗaukar matakin raba lardin da Kanada. Muhimmancinsa shi ne bayyana ra’ayin masu kaɗa ƙuri’a kan batun da ya daɗe yana haifar da muhawara a siyasar Alberta.

Lardin Alberta na daga cikin muhimman wuraren samar da man fetur a Kanada, kuma batun dangantakarsa da gwamnatin tarayya ya daɗe yana jawo muhawara kan tattalin arziki, iko da yadda ake tafiyar da albarkatun ƙasa.

By ukarofi

Leave a Reply