
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Laraba jam’iyyar APC ta sake fitar da wani jaddawali inda ta faɗaɗa jagoranci da mambobin kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu/APC na zaɓen 2027 (PCC).
Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar, Felix Morka ne ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar, wadda a ciki jam’iyyar ta ce an samu ƙarin naɗe-naɗe a rassan kwamitin daban-daban domin tabbatar da ingancin harkokinsa. Jam’iyyar ta jaddada ƙoƙarinta na tabbatar da bunƙasa harkokin shirye-shirye acikin rassan kwamitin yayin da shirin tunkarar babban zaɓen 2027 ya yi nisa.
Jaddawalin na yanzu an gina shi ne kan salon da aka fitar da fari a Agusta, 2026, wanda aka yi ƙoƙarin faɗaɗa ofisoshinsa ta hanyar ƙara waɗansu muƙamai da yin wasu muhimman gyare-gyare. Jaddawalin farko ya nuna cewa Shugaba President Tinubu shi ne shugaba, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da Shugaban APC na Ƙasa Farfesa Nentawe Yilwatda, a matsayin mataimaka shugaba, tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata Abdulaziz Yari shi ne darakta-janar, sai Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma a matsayin sakatare.
Jaddawalin da aka sabunta a tsakiyar Oktoba, 2026 ya faɗaɗa tsarin kwamitin wajen haɗawa da ‘yan tafiyar “rainbow coalition”, wanda ya janyo sanya wasu jiga-jigan ‘yan siyasa a wajen APC domin maslahar nasarar jam’iyyar. Cikin waɗanda aka ƙara a jaddawalin akwai Ministan Abuja, Nyesom Wike a matsayin kodinetan yaƙin neman zaɓe na Jihar Ribas da FCT; Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, appointed matsayin kodinetan Osun; da kuma Gwamnan Anambra, Chukwuma Soludo a matsayin kodinetan Jihar Anambra da dai sauransu.
A ranar 14 g Oktoba, 2026 ne dai aka ƙaddamar da kwamitin a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. Jaddawalin na ranar Laraba cigaba ne ga bin hanyoyin faɗaɗa kwamitin da ƙarin jagorori da mambobi domin ƙarfafa shirin APC a faɗin Nijeriya da matakin wayar da kan al’umma daga tushe gabanin zaɓen na 2027.
