Shirin ciyo bashin biliyan $21.7 don zuba jari ne ba kashewa ba, inji Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta kare yunƙurinta na ciyo bashin Dala biliyan 21.7 da Shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar Dokokin Ƙasa don neman amincewarta a kai, inda ta ce za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajen zuba jari a lamuran inganta ƙasa a madadin kashewa.

Ministan Kuɗi da Tattali, Mista Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan zaman Majalisar Zartarwar Tarayya (FEC) da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, ranar Laraba, 28 ga Oktoba, 2026. Oyedele, wanda ya bayyana haka yayin bayar da amsa game da koken al’umma da jagororin siyasa kan matakin, ya ce hakan shirin zuba jari ne na tsawon shekaru biyar a madadin rage adadin ainihin kuɗaɗen domin gajeren zango.

Ya bayyana cewa, biliyan $10.6 daga ciki an ware ne domin muhimman ayyukan ababen more rayuwa, ciki har da babbar hanyar Sakkwato zuwa Badagry, babban titin Legas zuwa Kalaba da layin dogo na Kano zuwa Kaduna.

Ministan ya ƙara da cewa sama da biliyan $7.9 na kuɗaɗen, za a karɓo su ne daga cibiyoyin kuɗaɗen ƙasashe daban-daban, ƙarƙashin jagorancin biliyan $5 daga Babban Bankin Duniya, a matakin kaso 2.1 na riba (interest). Ya ce, za a ware Dala biliyan 3.3 domin ga ayyukan gwamnatocin jihohi, da wani ƙarin biliyan $1.45 ga Babban Birnin Tarayya Abuja. “A ciyo bashin kuɗi don a kashe illa ce, amma aro N1 don gina muhimman kadarorin ci-gaba na sama da N1 abu ne da zai samar da arziƙi mai amfani ga ƙasar,” inji Ministan.

Kazalika, Oyedele ya bayyana wasu muhimman al’amuran farfaɗowar harkar tattali ta hanyar samar da shirye-shirye da gwamnatin ta yi, waɗanda suka haɗa da raba jimillar Naira biliyan 372.6 ta Shirin Bayar da Lamunin Karatu ga Ɗaliban Manyan Makarantu na Ƙasa (NELFUND) ga sama da ɗalibai miliyan 1.5; raba sama da Naira biliyan 600 ga magidanta don rage raɗaɗin matsin tattali da ƙoƙarin faɗaɗa shirin zuwa isarwa ga magidanta miliyan 15; da samar da bashi mai ruwa a matakin ƙasa da kaso 10 ga ƙananan ‘yan kasuwa sama da 800,000 daga Bankin Masana’antu (BOI).

Har ila yau, ya ce FEC ta amince da tsarin aiwatarwa na kwana 90 da Majalisar Tattalin Ƙasa (NEC) ta samar da kuma kiyaye horon a harkar kasafi ta yadda zai amfani ƙasa da al’umma da aka tsara shirin domin su.

By Babaji

Leave a Reply