NAFDAC ta lalata magungunan bogi a Lafia

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa, NAFDAC, ta lalata magungunan bogi da kayayyakin da suka lalace na kimanin Naira biliyan 8 da aka ƙwace daga shagunan magunguna da sauran kasuwanni a faɗin yankin Arewa ta tsakiya.

Da take magana a wajen aikin lalata kayayyakin a Lafia a ranar Alhamis, Darakta Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye ta bayyana sayar da irin waɗannan abubuwa ga ‘yan ƙasa a matsayin babbar barazana ga rayuwar ɗan Adam.

Adeyeye, wacce mataimakin darakta na NAFDAC bincike da tilastawa, yankin Arewa ta tsakiya Mista Joseph Edor, ya wakilta a wajen aikin ta ce an ƙwace kayayyakin ne daga masana’antu, masu shigo da su da masu rarrabawa domin kare lafiyar ‘yan ƙasa.

Darakta Janar ta NAFDAC ta ce, “Yana da muhimmanci a lura cewa shigowa da rarrabawa da sayar da kayayyakin bogi ga marasa lafiya na wakiltar babbar barazana ga rayuwar ɗan Adam. A yau, muna shaida lalata nau’o’in kayayyaki daban-daban da aka ƙayyade da kimanin daraja ta Naira biliyan 8. Waɗannan kayayyakin sun haɗa da magunguna, abinci, kayan kwalliya, ko dai an ƙwace su ko kuma kamfanoni masu bin doka, ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba ko ƙungiyoyin kasuwanci suka miƙa su da kansu.

“Lalata waɗannan kayayyakin zai hana a sake shigar da su cikin tsarin rarrabawa.”

Yayin da ta tabbatar cewa NAFDAC tana yin duk abin da ke cikin ikonta don tabbatar da cewa magunguna masu lafiya da kayayyaki masu kyau kaɗai ake sayarwa ga ‘yan ƙasa, Adeyeye ta nemi goyon baya da haɗin kai na jama’a don taimaka mata ta kawar da kasar daga magungunan bogi da kayayyaki.

A cikin saƙonnin fatan alheri, masu ruwa da tsaki daga ɓangaren lafiya, ƙungiyoyin lafiya da kuma hukumomin tsaro sun yaba wa NAFDAC da hukumomin tsaro a yankin saboda ƙoƙarin su wajen yaƙi da magungunan bogi da kayayyakin da suka lalace, kuma sun tabbatar musu da ci gaba da goyon baya da haɗin kai wajen tilasta hukunci ga ‘yan ƙasa masu laifi.

Yayin da suke gargaɗin masu saye da su dinga duba kwanan wata, adiresoshin da suka dace da lambar NAFDAC a kan magunguna da sauran abubuwan da ake cinyewa, masu ruwa da tsaki sun yi kira ga mazauna yankin da su haɗa kai da ma’aikatan hukumar kuma kada su riƙa ganin su a matsayin abokan gaba.

Wasu daga cikin ayyukan da aka gudanar a lokacin aikin lalata kayayyakin sun haɗa da lalatawa da kona kayayyakin da aka ƙwace da sauran su.

By ukarofi

Leave a Reply