
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis, 29 ga Oktoba 2026 Gwamnatin Tarayya ta hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC), ta gurfanar da Frins Matthew Adeniyi Adeyemi, wanda aka kira da Darakta-Janar na Hukumar bogi ta Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) a Babbar Kotun Birnin Tarayya, Abuja.
An gurfanar da Adeyemi ne a gaban Mai Shari’a Yusuf Halilu da ke zama a Maitama a Abuja bisa tuhume-tuhume guda 22 masu alaƙa da ƙaryar bayar da bayanai, ƙaryar zama ma’aikacin gwamnati, da zargin mallakar sama da Naira biliyan 27 domin kafa hukumar da kuma biliyan N3.8 ga ƙwadagon ma’aikata. A bayanan da ke cikin ƙarar, ICPC ta yi zargi Adeyemi da karɓar jimillar biliyan 30.8 daga asusun gwamnati ta hanyar bayar da bayanan ƙarya da aka danganta da Ministan Kuɗi da Tattalin Arziƙi.
Masu ƙarar sun yi zargin cewa a ranar 8 ga Maris, 2024 a Abuja, Adeyemi ya fitar da wata wasiƙa ta bogi mai lamba; SH/COS/209/A/3456 da kwanan wata 8 ga Maris, 2024, da aka ce wai Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya sanya wa hannu ko ya fitar da ita. A cewar ƙorafin, takardun suna nuna tabbacin naɗa Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na PFIPC da nufin ya zama sahihi kuma hakan ya ba shi damar amfani da kayayyakin ofishin gwamnati a Farfajiyar Sakatariyar Tarayya da ke Phase II.
Haka kuma ICPC ta yi iƙirarin cewa Adeyemi ya fitar da wata takardar bogi da ke nuna cewa shi ne darakta-janar na PFIPC da nufin samun amincewar cibiyoyin gwamnati da halascin gudanar da ayyukansa na damfara. Sannan, an zarge shi da fitar da wata takardar ƙarya mai taken “Re: Request for Approval of Self-Accounting Status”, da ya aike wa Akanta Janar na Ƙasa (AGF), domin bai wa PFIPC da ba ta wanzuwa damar shiga sahun masu aiki da tsarin rahoton kuɗaɗen gwamnati.
Kazalika, an zargi mutumin da shirya wasu takardun ƙarya da aka aike wa Darakta-Janar na Hukumar kula da Ci-gaban Fasahar Sadarwa (NITDA) domin samar da adireshin yanar gizo ga hukumar.
Har ila yau, masu ƙarar suna tuhumar Adeyemi da bayar da N210,000 ga wani Aminu Abdullahi, wanda Mataimakin Babban Jami’in Gudanarwa ne a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), da aka yi zargin an yi haka ne domin a ba wa PFIPC ofishi ba tare da sahalewa ba a hukumance. An kuma zarge shi da bai wa wani jami’i N300,000 a Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tattali, Ogaba Harry da manufar a samar masa da motoci biyu – Prado Jeep da Land Cruiser.
ICPC ta yi zargin a ranar 28 ga Yulin 2025, Adeyemin ya karɓi Naira miliyan 20 daga wajen Darakta-Manaja na Kamfanin Divine Dopacy Nigeria Litinin, Oyekunle Gbenga, a matsayin bashin kuɗin wasu ayyuka ta iƙirarin ƙarya. Ta ce, kuɗin na da alaƙa da kwangilar biliyan N2.8 da PFIPC ta bayar domin aikin siyan kayan kujeru da lantarki da kuma kwaskwarima ga gidan da aka ce gwamnati ce ta ba Adeyemi a hukumance.
ICPC ta ce, baki ɗaya waɗannan zarge-zarge an aikata su ne a tsakanin 2024 da 2026. A cewarta, aikata su saɓa wa hukunce-hukuncen Dokokin Ƙasa ne kamar haka:” Sections 364, 366 and 132 of the Penal Code, Cap. 532, Laws of the Federation of Nigeria (Abuja) 1990; Section 1(1)(a) of the Advance Fee Fraud and Other Fraud Related Offences Act, 2006, punishable under Section 1(3) of the same Act; and Section 9(a) of the Corrupt Practices and Other Related Offences Act, 2000, punishable under Section 9(b) of the same Act,” kamar yadda jaridar NewsPointNigeria ta wallafa.
Saidai, bayan an karanta wa Adeyemi waɗannan tuhume-tuhume, ya musanta baki ɗayansu a kotun. Bayan haka ne lauyar masu ƙara Fatima Bardi ta buƙaci kotun da ta sanya ranar da za a fara zaman shari’a domin bai wa masu ƙarar damar bayar da gamsassun hujjoji akan ƙorafe-ƙorafen da suka shigar kan Adeyemi.
Yayin da lauyan Adeyemi, Ibrahim Angulu ya nemi da a bayar da belin wanda yake karewa kan tsare shi na tsawon lokaci (kwana 155) da ƙalubalen lafiya da yake fuskanta, Mai Shari’a Halilu ya umarci da ya gabatar da hakan a rubuce. Daga nan ne alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 9 ga Nuwamba, domin fara shari’ar da kuma yiwuwar hukunci kan neman belinsa.
