Sanata Babba Kaita ya yi ta’aziyar kisan Sheikh Masussuka a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Sanata Ahmad Babba Kaita ya aika da ta’aziyyar sa ga iyalai, ‘yan uwa, abokan arziki da ɗimbin magoya bayan Sheikh Yahaya Masussuka wanda ‘yan bindiga suka harbe Talata 27/10/2026 a gidan sa da ke garin Dutsin-Ma, jihar Katsina.

Sanata Ahmad Babba Kaita ya kuma roƙi Allah da ya karɓi shahadar mamachin ya ba iyalan sa haƙurinrashin.

Sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ɗan takarar Malam Ahmed Abubakar, Sanata Babba Kaita ya yi nuni da cewa kisan shehin malamin ya ƙara nuna gazawar gwamnati mai ci tun daga matsayin jiha har sama wajen yaƙi da ta’addanci.

Ya kuma koka da yanda ita gwamnatin ta maida ran ɗan Najeriya ba a bakin komi ba.

Ɗan takarar gwamnan ya ƙara kira ga al’ummar jihar Katsina da ma ƙasa baki ɗaya musamman waɗanda za su yi zaɓen 2027 da su tabbatar da sun zabi adalan shugabanni masu gaskiya da sanin yakama, waɗanda ba duniya suka sa a gaba.

By ukarofi

Leave a Reply