2027: Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu saboda sauye-sauyen tattalin arziki – Wike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shekarar 2027, yana mai cewa gwamnatin shugaban ta nuna ƙarfin hali wajen aiwatar da wasu sauye-sauyen tattalin arziki masu ƙarƙaƙiya.

Wike ya yi wannan kira ne ranar Litinin, yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na gamayyar siyasa ta Rainbow Coalition, da aka gudanar a ƙaramar Hukumar Eleme ta Jihar Ribas. Ya buƙaci mazauna yankin da su mara wa Tinubu baya, tare da zaɓen ’yan takarar da gamayyar ta amince da su.

Ministan ya kawo cire tallafin man fetur a matsayin misali na yadda Tinubu ya nuna jajircewa wajen ɗaukar matakan da ba su da sauƙi, duk da wahalhalun tattalin arziki da ’yan Nijeriya ke fuskanta.

Ya bayyana cewa wannan mataki ya ƙara yawan kuɗaɗan da ake ware wa gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi, lamarin da ya ba su ƙarin damar biyan nauyin da ke kansu da kuma aiwatar da ayyukan raya ƙasa. “Mun san halin da ’yan Nijeriya suke ciki, amma muna da yaƙinin cewa abubuwa za su kyautata. Abu mafi muhimmanci shi ne, mun san yadda ƙasar nan take a baya,” inji shi.

Wike ya jaddada cewa shugabanci nagari yana buƙatar ƙarfin hali wajen ɗaukar matakan da ba lallai jama’a su so ba a lokacin da aka fara aiwatar da su, amma za su amfani ƙasa a nan gaba. Ya ce bai kamata shugabanni su guji yanke hukunci mai wahala saboda tsoron suka ba.

Ya bayyana cewa tsarin biyan tallafin man fetur na baya ya kasance babban nauyi ga kuɗaɗen gwamnati, wanda ya rage mata ƙarfin biyan hakkokin ma’aikata, ’yan fansho da sauran hukumomin gwamnati. Duk da cewa ya amince sauye-sauyen da aka aiwatar ba su magance dukkan matsalolin tattalin arzikin ƙasar ba, Wike ya buƙaci ’yan Nijeriya su yi haƙuri, yana mai nuna kyakkyawan fata cewa yanayin rayuwa zai inganta nan gaba.

Da yake magana kan lokacin da yake gwamnan Jihar Ribas, Wike ya tuna yadda gwamnatinsa ta ci gaba da gudanar da manyan ayyukan gina gadojin sama, duk da sukar da ake yi mata da kuma matsalolin wucin gadi da ayyukan suka haifar ga kasuwanci da zirga-zirgar ababen hawa. Ya ce waɗannan ayyuka sun nuna muhimmancin shugabanni su amince da wasu ƙananan matsaloli na ɗan lokaci idan hakan zai samar da ci gaba mai ɗorewa a nan gaba.

Ministan ya kuma buƙaci masu zaɓe su binciki tarihin ayyukan ’yan siyasar da ke neman mukaman gwamnati, yana mai gargaɗin kada su miƙa makomar ƙasar ga mutanen da ya bayyana a matsayin masu caca da siyasa. “Kada ku miƙa makomarku ga masu caca da siyasa,” inji shi.

Wike ya danganta wasu daga cikin zaɓin siyasa da aka yi a zaɓen shekarar 2023 da ƙarancin sahihan bayanai da kuma farfagandar siyasa. Saboda haka, ya buƙaci mazauna Jihar Ribas su yi zaɓe bisa cikakken sani da fahimta a zaɓe mai zuwa. Ya ce an shirya taron ne domin tattaunawa da shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, mata da matasa kan makomar Jihar Ribas da Nijeriya baki ɗaya.

Tsohon gwamnan ya kuma kare gamayyar siyasa ta Rainbow, wadda ta haɗa mambobin Jam’iyyar PDP, Jam’iyyar APC da wasu jam’iyyun siyasa. Ya ce an kafa gamayyar ne domin inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Jihar Ribas.

Wike, wanda ya bayyana kansa a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin ƙasa na PDP, ya ce mambobin gamayyar sun amince su haɗa kai, tare da mara wa ’yan takarar da za su tsaya takara ƙarƙashin inuwar APC a zaɓen shekarar 2027 baya.

Ya yi kira ga mazauna jihar da su goyi bayan ƙoƙarin sake zaɓen Tinubu, da kuma ’yan takarar da gamayyar ta amince da su domin neman kujerar gwamna, kujerun majalisun dokoki da sauran muƙaman zaɓe. “Ba ma son Ribas ta zama kogin jini. Ba ma son Ribas ta zama kogin harbe-harbe. Manyan jam’iyyun siyasa biyu a jihar nan su ne APC da PDP. Sun haɗa kai da sauran jam’iyyun siyasa domin cewa, ‘A samu zaman lafiya a Jihar Ribas, a samu ci gaba da haɗin kai,’” inji shi.

Wike ya jaddada cewa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jihar Riba da zaɓaɓcun wakilan al’umma yana da matuƙar muhimmanci wajen inganta ci gaban jihar.

Da yake bayyana Eleme a matsayin yanki mai muhimmancin tattalin arziki ga Nijeriya, ya buƙaci mazauna yankin su yi amfani da ƙuri’unsu cikin hikima, tare da goyon bayan tsarin siyasar da yake ganin zai samar da kwanciyar hankali da ci gaba. Taron ya samu halartar shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai, mata, matasa da wakilan jam’iyyun siyasa da suka shiga haɗakar Rainbow.

By ukarofi

Leave a Reply