Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa Maso Gabas, Operation Haɗin Kai (OPHK), ta ce ta kashe mayaƙa 16 da ake zargin ’yan ƙungiyar ISWAP ne a wasu hare-haren sama da aka kai kan maboyarsu guda uku a yankin Tunbunma da ke kudancin Tafkin Chadi.
Muƙaddashin Jami’in Yaɗa Labaran rundunar, Kyaftin Mohammed Goni, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa, inda ya ce an kai hare-haren ne tsakanin ƙarfe 1:00 zuwa 2:00 na dare a ranar 26 ga Oktoba, 2026.
Ya ce an gudanar da farmakin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu manyan jagorori da mayaƙan ƙungiyar na cikin wuraren, inda aka yi amfani da makamai na sama da na ƙasa.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito sanarwar na cewa, hare-haren wani ɓangare ne na ci gaba da matsin lamba kan ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.
Rundunar ta jaddada aniyarta ta kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci da dawo da zaman lafiya a Arewa Maso Gabashin Nijeriya, tare da kira ga jama’a da su riƙa kai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai cikin gaggawa domin taimaka wa ayyukan yaƙi da
