Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Hukumar Binciken Manyan Laifuffuka ta Amurka (FBI) ta ce ta kama mutum tara a Nijeriya bisa zargin hannu a cibiyoyin damfara ta intanet, yayin da aka gano kuɗaɗen da yawansu ya kai dala miliyan 11 da ake ganin za a iya ƙwacewa a ƙasashe daban-daban.
Daraktan FBI, Kash Patel, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 25 ga Oktoba, 2026, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, inda ya ce an kuma ƙwace na’urorin laturoni guda 53 a yayin samamen mai suna Operation Blackout.
Patel ya ce cibiyoyin damfarar suna yaudarar mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, suna ƙwace musu kuɗaɗensu, har ma da dukiyar da suka tara tsawon rayuwarsu.
Ya ce masu gudanar da ayyukan damfarar suna aiki a ƙasashe daban-daban, suna zaton cewa ba za a iya hukunta su ba saboda nisan da ke tsakaninsu da ƙasashen da suke cutar da mutanensu.
Sai dai ya yi gargaɗin cewa hukumomin tsaro za su ci gaba da bin sawun waɗanda ke damfarar Amurkawa daga ƙasashen waje, domin gurfanar da su a gaban shari’a.
Patel ya kuma miƙa godiyarsa ga hukumomin tsaron Nijeriya da abokan hulɗar FBI da ke birnin Landan na Birtaniya bisa haɗin kan da suka bayar wajen gudanar da aikin.
Binciken ya nuna cewa kamen mutanen tara a Nijeriya na daga cikin wani gagarumin samame na haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na ƙasashe daban-daban da kamfanonin fasaha, domin tarwatsa cibiyoyin damfara da ke aiki a Afirka ta Yamma.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta fitar a ranar 13 ga Oktoba, 2026, ta ce an kama mutane 28 a Nijeriya da Ghana a wani aikin haɗin gwiwa da aka gudanar a makon da ya fara ranar 6 ga Oktoba.
Daga cikin waɗanda aka kama, tara na Nijeriya ne, yayin da aka kama wasu 19 a ƙasar Ghana, inda jami’an tsaro suka kuma ƙwace na’urorin laturoni 303.
A Ghana, hukumomin tsaro sun gano mutane 117 da ake zargin an yi safarar su zuwa wuraren da ake gudanar da damfarar, waɗanda ake shirin mayarwa Nijeriya. Haka kuma, an gano wasu mutane 89 da aka damfara, waɗanda suka yi asarar kusan dala miliyan 8.3.
Ma’aikatar Shari’ar Amurka ta ce samamen ya shafi cibiyoyin damfara da ke amfani da sunan jami’an tsaro wajen yaudarar mutane, yi musu barazana ta intanet, da kuma damfarar masu zuba jari a harkokin kuɗaɗen intanet, musamman na cryptocurrency.
A yayin aikin, kamfanonin fasaha sun taimaka wajen gano tare da daƙile ayyukan damfarar a shafukan intanet.
A cewar Ma’aikatar Shari’ar Amurka, an cire sama da asusu, shafuka da ƙungiyoyin sada zumunta miliyan 3.7 da ake zargin ana amfani da su wajen damfarar mutane a Amurka, Birtaniya da sauran ƙasashe.
Hukumomin tsaro da kamfanonin sun kuma gano kuɗaɗen da yawansu ya haura dala miliyan 11 da ake ganin za a iya sanya takunkumi a kansu ko ƙwacewa.
Sai dai ba a tabbatar da cewa an ƙwace duk waɗannan kuɗaɗen ba, kuma ba a bayyana adadin kuɗin da ke da alaƙa kai tsaye da ayyukan da aka gano a Nijeriya ba.
Aikin ya haɗa da hukumomin tsaro na Amurka, Birtaniya, Nijeriya da Ghana, tare da wasu hukumomi da kamfanonin fasaha na ƙasashe daban-daban.
Hukumomin sun ce za su ci gaba da haɗa kai domin tarwatsa ƙungiyoyin da ke amfani da intanet wajen damfarar mutane da kuma gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan a gaban shari’a.
