Wasu jiga-jigan gwamnatin Buhari sun yi wa Tinubu zagon ƙasa – Akande

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo, Laolu Akande, ya zargi wasu jiga-jigan gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da yi wa Shugaba Bola Tinubu zagon ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a 2022.

Akande, wanda ya bayyana hakan a wata hira da tashar Symfoni Tɓ, ya ce wasu daga cikin mutanen sun fi son tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

Ya ce duk da irin gudummawar da Tinubu ya bayar wajen kafa APC da nasarorin zaɓenta, an mayar da shi saniyar ware a lokacin mulkin Buhari daga 2015 zuwa 2023.

A cewarsa, ya shaida yadda ake ware Tinubu a wasu tarukan siyasa, amma ya ci gaba da haƙuri har zuwa lokacin da ya samu damar cimma burinsa na shugabancin ƙasa.

Akande ya kuma ce wasu daga cikin jiga-jigan sun yi watsi da sunayen mutanen da Tinubu ya gabatar domin naɗin ministoci, ciki har da Dele Alake da Wale Edun, domin nuna cewa ba shi ne ke da ikon tantance naɗe-naɗen gwamnati ba.

Ya ƙara da cewa sauya fasalin kuɗin Naira da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya yi gabannin zaɓen 2023 ya yi barazana ga burin Tinubu na zama shugaban ƙasa, sai dai ya nuna ƙwarewa wajen tunkarar matsalar.

A zaɓen fidda gwanin APC na watan Yunin 2022, Tinubu ya doke Ahmad Lawan, Osinbajo da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, inda ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.

By ukarofi

Leave a Reply