Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
ɗalibai 64 na Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati da ke Batagarawa, a Jihar Katsina, sun kwanta asibiti bayan sun nuna alamun rashin lafiya sakamakon shan magungunan da aka ba su yayin wani shirin yaƙi da cutar fitsarin jini, wato Bilharzia.
An garzaya da ɗaliban zuwa Babban Asibitin Ahmadi Rimi da Asibitin Mata da Yara na Turai Yar’Adua da ke Katsina, bayan sun fara amai, jin raɗaɗin ciki da kuma jiri.
Lamarin ya jefa iyayen ɗaliban da sauran al’ummar makarantar cikin fargaba, musamman bayan rahotannin cewa an kai wasu daga cikinsu asibiti a sume.
“An kawo su asibiti a sume,” in ji Daraktan Babban Asibitin Ahmadi Rimi, Dakta Auwal Sani.
Sai dai ya ƙara da cewa ɗaliban da abin ya shafa suna samun sauƙi sakamakon jinyar da ake yi musu.
Wani mahaifi da ya ziyarci ’ya’yansa a asibiti ya tabbatar wa wakilin jaridar cewa suna samun sauƙi.
Wasu daga cikin ɗaliban, Abubakar Muhammad Khairi da Hassan Muhammad, sun bayyana cewa an ba su magungunan ne bayan an auna tsayinsu.
A cewarsu, adadin ƙwayoyin maganin da aka ba kowane ɗalibi ya bambanta. An ba wasu ƙwayoyi uku, wasu biyu, yayin da aka ba wasu ƙwaya ɗaya, bisa la’akari da tsayinsu.
Sai dai har yanzu ba a fayyace ko tsayin ɗaliban ne kaɗai aka yi la’akari da shi wajen ƙayyade adadin maganin da za su sha ba, ko kuma an yi la’akari da wasu ƙa’idojin lafiya.
Wani mahaifi, Malam Ma’aruf Sani, wanda ya ziyarci ’ya’yansa da abin ya shafa a asibiti, ya ce sun warke daga illolin da suka fuskanta.
Kwamishinan Ilimin Firamare da Sakandare na Jihar Katsina, Yusuf Sulaiman Jibia, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce dukkan ɗaliban da abin ya shafa sun warke, kuma ana shirin mayar da su makaranta.
“ɗaliban da abin ya shafa sun warke sarai, kuma muna shirye-shiryen mayar da su makaranta,” inji Jibia.
Ya bayyana cewa hukumomin kula da lafiya a matakin farko ne suka gudanar da aikin bayar da magungunan, tare da haɗin gwiwar ƙaramar Hukumar Batagarawa.
Kwamishinan ya tabbatar wa iyaye da mazauna yankin cewa babu abin da zai sa su firgita, yana mai cewa gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike domin gano abin da ya faru da kuma musabbabin matsalar.
Jibia ya ƙara da cewa ana ba ɗaliban abinci kafin a mayar da su makaranta.
Bilharzia, wadda aka fi sani da schistosomiasis, cuta ce da wasu ƙwayoyin halitta masu kama da tsutsotsi ke haddasawa. Ana iya kamuwa da ita ta hanyar taɓa ko shiga ruwan da ke ɗauke da ƙwayoyin cutar, musamman a wasu wuraren da ruwan ya gurɓata.
Sai dai har yanzu ba a gano ainihin dalilin da ya sa ɗaliban suka fuskanci waɗannan matsalolin lafiya ba.
Ya zuwa lokacin kammala rahoton, babu wani sakamakon bincike a hukumance da aka fitar wanda ya tabbatar da ko matsalar ta samo asali ne daga maganin, adadin da aka ba ɗaliban, ko kuma wasu dalilai.
Jami’ai sun bayyana cewa ana gudanar da shirye-shiryen bayar da magungunan rigakafi a al’ummomin da cutar ta fi shafa domin rage yaɗuwarta da illolinta.
