Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Da safiyar yau Litinin, an samu wani mummunan lamari a daidai Gidan Kano, kusa da garin Danbaza, a ƙaramar hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, wasu ‘yan bindiga, sun yi kwanton ɓauna ga wata mota ta gwamnati mallakin hukumar sufuri ta Jihar Zamfara (Zamfara State Transport Authority) wadda ke ɗauke da jami’an tsaro da ke kan hanyarsu ta zuwa wajen gudanar da aiki na musamman (Special Duty) daga Sokoto zuwa Zamfara.
Rahotanni daga wajen da lamarin ya faru sun tabbatar da cewa maharan sun buɗe wuta sosai kan motar.
A sakamakon wannan mummunan harin, rahotanni sun nuna cewa jami’an ‘yan sanda biyar ne suka rasa rayukansu nan take, yayin da wasu jami’an da kwanansu bai ƙare ba suka samu mummunan raunuka sakamakon harbin bindiga.
Wannan al’amari ya ƙara jefa al’ummar Jihar Zamfara cikin jimami da alhini, duba da irin yadda jami’an tsaro ke sadaukar da rayukansu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Hakazalika har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, duk ƙoƙarin zantawa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Zamfara DSP Yazid Abubabakar ya ci tura.
