Shugaban ƙaramar hukumar Kaura Namoda ya tsallake rijiya da baya hannun fusatattun matasa a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ruɗani ya ɓarke a yau Litinin a garin Ƙaura Namoda yayin zaɓen fidda gwanin kujerar Sanata na Zamfara ta Arewa a ƙarƙashin jam’iyyar APC, inda shugaban ƙaramar hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Haidara, ya tsallake rijiya da baya a hannun wasu fusatattun matasa.

Rahotannin da aka samu daga wurin taron sun nuna cewa lamarin ya faru ne lokacin da Hon. Haidara yake jawabi ga wakilai da matasa a filin zaɓen, yana mai kira gare su da su zaɓi Sanata mai ci, Sanata Sahabi Ya’u Ƙaura.

Sai dai matasan da ke wurin, wadanda mafi yawansu magoya bayan abokin takararsa ne, Sanata Tijjani Yahaya Kaura (OD), sun nuna adawa da kiran nasa kuma suka dage cewa sai sun goyi bayan ɗan takarar nasu.

Shaidun gani da ido sun ce lamarin ya rikiɗe zuwa hargitsi nan take, inda fusatattun matasan suka fara ihu da ƙoƙarin kai hari kan shugaban ƙaramar hukumar bisa abin da suka bayyana a matsayin nuna son kai da ƙoƙarin ƙaƙaba musu ɗan takara.

Ceton Hon. Mannir Haidara ya samu ne sakamakon gaggawar da jami’an ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da ke wurin suka yi, inda suka yi sauri suka kuɓutar da shi daga hannun taron matasan tare da ficewa da shi daga wurin.

Zaɓen fidda gwanin, wanda yake takara ne tsakanin Sanata Sahabi Ya’u da Sanata Tijjani Yahaya OD, da Dr. Sani Abdullahi Shinkafi domin tikitin Zamfara ta Arewa, yana gudana a ƙananan hukumomin Kaura Namoda, Birnin Magaji, Shinkafi da Zurmi.

Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, an dawo da zaman lafiya, amma jami’an tsaro sun ƙara yawa a wurin da ake gudanar da zaɓen.

By ukarofi

Leave a Reply