Daga AISHA ASAS
Mai karatu, barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na jarida mai farin jini Blueprint Manhaja, shafin da muke haɗuwa domin fahimtar al’amuran kwalliya, tare da duba yadda za mu riƙa ƙawata kanmu ba tare da mun manta da lafiyar jikinmu ba.
A yau, za mu yi magana ne kan wani sinadari na kwalliya da ya zama tamkar abokin zama ga mata da dama, musamman waɗanda suke son ganin fuskarsu ta yi kyau, ta yi laushi a gani, kuma ta kasance da launin da ya yi daidai a ko’ina. Wannan kayan kwalliya shi ne foundation.
A wurin wasu mata, fita ba tare da shafa foundation ba tamkar fita ne ba tare da an kammala shirin kwalliya ba. Wasu kuwa suna amfani da ita ne idan za su halarci biki, ɗaurin aure, liyafa ko wani muhimmin taro. Akwai kuma waɗanda suke amfani da shi a kullum, ko da za su fita kasuwa ne ko zuwa wurin aiki. Ga waɗannan mata, foundation ba kawai wani abu ne da ake shafawa a fuska ba; yana taimaka musu su samu irin kamannin da suke so, ya ba su kwarin gwiwar bayyana a tsakanin jama’a, musamman idan suna son ɓoye wasu abubuwan da ba sa so a gani a fuskarsu.
Sai dai, a ƙarƙashin wannan kyakkyawar fuska da ake gani bayan an kammala kwalliya, akwai tambayoyi da ya kamata kowace mace ta yi wa kanta. Shin foundation yana da illa ga fata? Ko kuwa tsoron da ake nunawa game da ita ya wuce gaskiyar abin da masana lafiya suka tabbatar? Shin mace mai kurajen fuska za ta iya amfani da shi? Kuma shin duk foundation ɗin da ake sayarwa ya dace da kowace irin fata?
Domin amsa waɗannan tambayoyi, yana da muhimmanci mu fara fahimtar ainihin abin da foundation yake yi, kafin mu duba abin da masana suka gano game da amfaninsa da kuma matsalolin da ka iya tasowa sakamakon amfani da shi ba daidai ba.
Shin ko kin san cewa foundation ba foda kawai ba ne?
Idan aka ce foundation, wasu kan ɗauka ana magana ne kawai kan foda da ake shafawa a fuska. Amma a zahiri, foundation yana cikin kayan kwalliyar da ake amfani da su domin daidaita launin fuska da kuma rage bayyanar wasu alamomi a fata. Yana zuwa da nau’o’i daban-daban, ciki har da wanda yake ruwa, wanda yake mai kauri kamar man shafawa, da kuma wanda yake garin foda.
A cewar bayanin da Cibiyar Kula da Guba ta Amurka, wato National Capital Poison Center, foundation na iya ƙunsar sinadarai daban-daban, gwargwadon irin samfurin da aka ƙera. Daga cikin abubuwan da ake iya samu a wasu nau’o’insu akwai titanium dioɗide, zinc oɗide, kaolin da kuma wasu ma’adanai ko sinadarai da ke taimaka wa samfurin samun launinsa da kuma yadda yake zama a kan fata. Ba lallai ne dukkan foundation su ƙunshi waɗannan sinadarai iri ɗaya ba, domin tsarin ƙera su ya bambanta.
Babban aikinsa shi ne taimaka wa fuska ta samu launi mai daidaito, tare da rage bayyanar tabo, bambancin launin fata da wasu ƙananan alamomi. Wannan ya sa ake yawan amfani da shi a matsayin matakin farko na kwalliyar fuska, kafin a ƙara wasu kayan kamar concealer, foda ta kammalawa da sauran kayan ƙawata fuska.
Amma yana da kyau mace ta fahimci cewa foundation kayan kwalliya ne, ba maganin fata ba. Idan ya ɓoye kuraje ko tabo a lokacin da take fuskantar jama’a, hakan ba yana nufin ya warkar da kurajen ko ya kawar da tabon ba. Bambancin nan yana da muhimmanci, domin wasu mata kan yi amfani da kayan kwalliya wajen ɓoye matsalar fata, alhali matsalar tana ci gaba da kasancewa a ƙarƙashinta.
Me ya sa foundation ya zama abin so ga mata?
Za mu ci gaba.
