‘Yan sanda sun kama ƙasurgumin dillalin ƙwaya a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ‘yan sanda a Katsina sun sami nasarar kama wani ƙasurgumin dillalin ƙwayoyi ɗauke da ƙwayar Pregabalin 15,000 a garin Katsina.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da sanarwar haka,ya bayyana cewa sun kama Junaidu Rabi’u ɗan shekara 45 da haihuwa a babban kasuwar Katsina bayan samun bayanan sirri akan wanda ake zargi.

A bincike da suka gudanar DSP Abubakar Sadiq yace wanda ake zargi ya amsa laifin sa inda ya bayyana cewa wani mai suna Nafi’u zai iso ya amshi kayan a madadin wanda ake zargi ya kaisu wuraren da suka saba kaiwa.

A halin yanzu “yan sanda sun ƙara ƙaimi wajan kamo Nafi’u da suke nema ruwa a Jallo domin gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ‘yan sanda CP Ali Fage ya jinjina wa jami’an tsaron bisa nuna ƙwarewa da har ta kai su da kama wannan miyagun mutane.

CP Fage ya ƙara tabbatar wa al’ummar Katsina ƙoƙarin da rundunar ‘yan sanda na magance mayan laifuka a jihar ya kuma yaba da Irin gudummawa da jama’a ke ba jami’an tsaro a jihar wajen tabbatar da tsaro.

By ukarofi

Leave a Reply