
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawa ta bai wa majalisun dokokin jihohin da ba su kai ga amincewa da dokar kafa ‘yan sandan jihohi ba wa’adin zuwa ranar 15 Nuwamba, 2026 domin su bayar da ba’asinsu a game da al’amarin, inda ta yi gargaɗin cewa rashin yin hakan ka iya zama sanadin ƙin karɓar amincewarsu.
Hakan ya biyo bayan ba’asin da Jagoran Sanatoci, Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar yayin zamanta na ranar Laraba, inda ya ce 30 daga cikin majalisun jihohi 36 sun amince da kafa dokar bayan yi wa ta ƙasa kwaskwarima.
Duk da cewa amincewa 30 da aka samu sun wadatar na samun kaso biyu bisa uku a dokance na daga mafiya rinjayen majalisun jihohi 24, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya roƙi a ƙara lokaci ga sauran majalisu shidan da suka rage domin su bayyana matsayarsu, yana mai cewa gazawar haka ka iya sa a ƙi karɓar amincewarsu.
Majalisun jihohin da suka amince da dokar sun haɗa da na Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Borno, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Legas, Nasarawa, Ogun, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, Taraba, Yobe da kuma Zamfara.
