Daga JOHN D. WADA a Lafia
Gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya gudana a filin Lafia Square da ke Lafia babban birnin Jihar Nasarawa a jiya Laraba, inda mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ya isar da saƙo daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu ga mambobin jam’iyyar da magoya bayanta a jihar da kuma a faɗin ƙasar.
Shettima yace saƙon shugaban shi ne cewa dukkan mambobin APC da magoya bayanta su zaɓi dukkan ‘yan takarar APC tun daga sama har ƙasa kuma su yi watsi da batun zaɓen rainbow.
Saƙon ya samu ƙarfafa daga dukkan masu jawabi a yayin taron ciki har da gwamna Abdullahi Sule da darakta janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasar Abdulaziz Yari.
Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya buƙaci ‘yan jam’iyyar a wajen taron da su kasance masu biyayya ga jam’iyyar tare da tabbatar da cikakkiyar nasara ga APC a zaɓukan gama-gari masu zuwa ta hanyar zaɓen ‘yan takarar jam’iyyar a dukkan matakai, daga zaɓen shugaban ƙasa zuwa gwamna, majalisar tarayya da majalisar dokokin jiha.
Gwamna Abdullahi Sule a nasa ɓangaren wanda shi ne ko’odinetan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jihar kuma shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓe na Jihar ya kuma buƙaci magoya baya da su kasance da haɗin kai tare da yin aiki domin nasarar dukkan ‘yan takarar APC a jihar.
Yace Jihar Nasarawa za ta ba shugaba Tinubu da sauran ‘yan takarar APC gagarumar nasara idan mambobi suka ƙaurace wa rarrabuwar kawuna tare da zaɓen jam’iyyar kai tsaye.
A nasa ɓangaren darakta janar na yaƙin neman zaɓe, Abdulaziz Yari ya yi gargaɗi ga magoya baya kan raba ƙuri’unsu tsakanin jam’iyyu daban-daban, yana mai cewa zaɓen rainbow kawai yana raunana jam’iyyar ne kuma yana rage mata damar isar da ribar dimokuraɗiyya.
Ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar, ko’odinetoci da magoya baya a faɗin ƙananan hukumomi 13 da su wayar da masu zaɓe a rumfunan zaɓe don tabbatar da cikakkiyar nasara ga APC.
Taron ya samu halartar shugabannin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki da ‘yan takara da ƙungiyoyin mata da matasa da kuma magoya baya daga faɗin jihar da sauran su.
