Tinubu ya maye gurbin ciyo bashin biliyan $21.5 da shirin aro Dala 7.7bn

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa da ta dakatar da aiki akan buƙatar ranar 26 ga Oktoba na neman ta amince masa ciyo bashin Dala biliyan 20.52 da Yuro biliyan 1.045, tare da maye gurbinsa da shirinsa na karɓo aron Dala biliyan 7.7 domin toshe giɓin da aka samu a kasafin 2026.

Hakan na ƙunshe ne ciki wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Oktoba, wadda Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya karanta a ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026. Akpabio ya shaida wa ‘yan majalisar cewa sabuwar buƙatar ta soke ta farkon ta karɓo rancen $20.52bn da €1.045 a ƙasashen waje, wanda shugaban da fari ya nemi majalisar ta sahale masa.

Dala biliyan 7.7 ɓangare ne na shirin anso lamunin Naira tiriliyan 29.2 a ƙarƙashin Dokar Kasafi ta 2026 domin cike gurbin ragowar kuɗaɗen da ake buƙata, wanda aka ƙiyasta kan Naira tiriliyan 31.4. A cewar Shugaban, jimillar adadin da za a aro a ƙasashen waje ya kai tiriliyan N10.79, yayin da za a nemi tiriliyan N18.4 a cikin gida Nijeriya.

Ya bayyana cewa, za a samu kuɗaɗen wajen ne ta hanyoyin kuɗaɗe daban-daban, ciki har da ɓangaren Turai, cibiyoyin kuɗaɗe na ‘yan kasuwa da na gwamnatoci, asusun tallafin kuɗaɗe da wasu yarjejeniyoyin samar da kuɗi.

Shugaba Tinubu ya ce, za a yi amfani da kuɗaɗen ne wajena aiwatar da ayyukan raya ƙasa da shirye-shiryen da aka tsara gudanarwa ƙarƙashin Dokar Kasafi ta 2026 musamman kan muhimman al’amuran da suka shafi tattali. Ya zayyano kariya da tsaro, sufuri, noma, lantarki, ilimi da kiwon lafiya a matsayin ababen da za a fifita wajen aiwatar da lamunin.

By Babaji

Leave a Reply