Sojoji sun ƙwato makamai da babura 33 bayan ceto mutum 16 a Neja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun Sojin Nijeriya sun yi nasarar ceto mutane 16 da aka yi garkuwa da su tare da ƙwato wasu bindigu biyu ƙirar AK-47, boma-boman RPG uku da kuma babura 33 yayin wani atisaye akan ‘yan ta’adda a Jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa, atisayen, wanda aka gudanar a ranar 5 ga Nuwamba, 2026 ya kuma taimaka wajen ƙwato akwatin harsasai bakwai, tarin alburusai da kuma tsabar kuɗi Naira miliyan 4.1 bayan kwanton-ɓauna akan hanyoyin da ‘yan ta’adda suke zirga-zirga a yankin Ƙaramar Hukumar Kontagora da ke jihar.

Jami’an Birget ta 18 ta rundunar ne suka ƙaddamar da atisayen bayan samun wasu bayanan sirri dangane da zirga-zirgar ‘yan ta’adda daga Ƙaramar Hukumar Mashegu zuwa Rijiyan Nagwamatse a Kontagora, inda suka riske su bayan da fari sun sace wasu mutane.

A sanarwar da Mataimakin Daraktan Harkokin yaɗa Labaran birget ɗin na Riƙo, Adebayo Adewumi ya fitar, rundunar ta ce sojojin sun kuma halaka ‘yan ta’adda da dama da ba a iya ƙiyasce adadinsu ba yayin arangamar. Ya ce, an bayar da magani ga mutane goma sha shidan da aka ceto kuma tuni aka damƙa su a hannun hukumomin tsaron da suka dace domin sada su da iyalansu.

Rundunar ta ƙara da cewa, wannan ya nuna yadda dakarunta suke faɗaɗa ayyukansu na daƙile ta’addanci, wanda ya samu ne sakamakon tura ƙarin jami’ai a wurare masu fuskantar barazanar hare-hare da ƙarfafa ikonsa wajen tunkarar ƙalubalen tsaro.

By Babaji

Leave a Reply