Za mu dawo da buga jaridar Triumph kullum — Dawakin Tofa

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABa Kano

‘Malam Sunusi Bature Dawakin Tofa, Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamnatin Kano, wanda Gwamna Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunansa ga Majalisar Dokokin Kano domin tantance shi da niyyar naɗa shi a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kano, ya bayyana cewa babban burinsa idan ya samu wannan dama shi ne dawo da buga jaridar Triumph domin ta riƙa fitowa kullum kamar yadda take a baya.

Ya kuma bayyana aniyarsa ta kawo sababbin tsare-tsare na zamani a kafafen yaɗa labaran gwamnatin Kano, ciki har da Rediyo Kano da gidan talabijin na Abubakar Rimi Television (ARTV). Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan fitowa daga zauren Majalisar Dokokin Kano, a ranar Talatar da ta gabata, lokacin da yake ganawa da manema labarai a harabar majalisar da ke birnin Kano.

Tuni dai masana aikin jarida da tasirinta a siyasar duniya, gudanarwa da adana tarihi suka fara bayyana ra’ayoyinsu na cewa wannan mataki ya dace. Sun bayyana cewa jarida na da muhimmiyar rawa wajen adana tarihi, inda suka bayar da misalin wani lokaci da ɗaya daga cikin tsofaffin gwamnonin jihar Kano ya nemi a samo masa jawabin da ya fara yi bayan hawansa kujerar gwamna, lokacin da yake shirin sauka daga mulki.

An nemi jawabin a wurare daban-daban, ciki har da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da sauran hukumomin da ake sa ran za a samu bayanan a rubuce, amma aka rasa. Daga ƙarshe aka nemi jaridar Triumph, inda aka samu jawabin duk da cewa an kasa samunsa a hannun hukumomin da abin ya shafa. Wannan ya nuna irin muhimmancin jaridu wajen adana tarihi.

Haka kuma, an ruwaito tsohon Gwamnan Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, yana ba wa wasu masu magana a kafafen yaɗa labarai shawarar su riƙa faɗin gaskiya komai ɗacinta, tare da guje wa cin mutunci da ɓata sunan kowane ɗan siyasa.

A wani ɓangaren kuma, wani shahararren ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Sabitu Yahya Muhammad Jifatu, ya bayyana a wata hira da manema labarai cewa ya fi samun nutsuwa wajen tattaunawa da jarida fiye da sauran kafafen sada zumunta, domin a cewarsa, jarida tana buƙatar mutum mai ilimi wanda ba ya son yin magana ba tare da sanin abin da yake faɗa ba.

Waɗannan ra’ayoyi da sauran bayanai sun nuna irin tasirin jarida a rayuwar al’umma. Saboda haka, wannan fata da Dawakin Tofa ya bayyana abin a yaba ne, kuma ana fatan Allah Ya ba su ikon aiwatar da shi cikin gaggawa.

By ukarofi

Leave a Reply