Bayan tsawon shekaru a tsare, DSS ta wanke wasu ’yan Bayelsa huɗu daga zargin alaƙa da IPOB

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta saki wasu mutum huɗu daga jihar Bayelsa bayan ta kammala bincike tare da wanke su daga zargin kasancewa mambobin ƙungiyar IPOB. Hukumar ta kuma amince da biyan su diyyar Naira miliyan 20, wato Naira miliyan biyar ga kowane mutum.

Babban Daraktan hukumar DSS, Oluwatosin Adeola Ajayi, ne ya bayar da umarnin sakin mutanen tare da amincewa da biyan diyyar. Mutanen da abin ya shafa su ne Emele Uduma Ibe, Berefgagha Appah, Ondokeyilemi Aggry da Oyeinmokebebeton Aggry.

An kama mutanen ne a watan Mayun 2022 a garuruwan Sampou da Akeddei da ke ƙananan hukumomin Kolokuma/Opokuma da Sagbama, a jihar Bayelsa. Bincike ya nuna cewa wasu mambobin IPOB, waɗanda yanzu ake shari’a da su, sun yaudare su da cewa za su riƙa samun Naira dubu 100 duk wata a ƙarƙashin shirin afuwa na gwamnatin tarayya.

Lauyoyinsu, Deji Adeyanju & Partners, sun yaba wa hukumar DSS bisa matakin sakin mutanen da kuma amincewa da biyan su diyya. Da yake magana a madadin sauran mutanen, Emele Uduma Ibe ya bayyana ranar a matsayin mafi farin ciki a rayuwarsu, tare da cewa abin da ya faru ya zama babban darasi a gare su.

Tun bayan hawansa kujerar babban darakta a shekarar 2024, Ajayi ya bayar da umarnin sake duba shari’o’in sama da 300 da suka shafi ta’addanci, waɗanda ya gada daga tsoffin shugabannin hukumar. Sakamakon binciken ya taimaka wajen rage cunkoson da ke cibiyar tsare mutanen hukumar, inda adadin waɗanda ake tsare da su ya ragu zuwa kusan 100.

Hukumar ta kuma biya wasu mutane diyya bayan bincike ya tabbatar da cewa an yi musu kuskure. Daga cikinsu akwai wani ɗan kasuwa a Jos da aka biya Naira miliyan 20 tare da kuɗin jinya bayan jami’an DSS sun harbe shi bisa kuskure a jihar Plateau; Chineze Ozoadibe da aka biya Naira miliyan 10 sakamakon kama shi ba bisa ƙa’ida ba; Sunday Ifedi da aka biya Naira miliyan 10 bayan an wanke shi daga zargin alaƙa da IPOB; da Kenneth Okechukwu Nwafor da aka biya Naira miliyan biyar.

DSS ta kuma bayyana cewa za ta samar da tallafin kula da lafiyar kwakwalwa da ta jiki ga mutanen da abin ya shafa, tare da taimaka musu wajen komawa cikin al’umma.

Ajayi ya amince cewa hukumar DSS ma tana iya yin kuskure a yayin gudanar da ayyukanta, amma ya jaddada cewa idan aka samu irin wannan kuskure, wajibi ne a gyara shi tare da biyan diyya ga waɗanda abin ya shafa. Ya ce amincewa da kuskure da kuma ɗaukar matakan gyara na taimaka wa hukumar inganta ayyukanta tare da bin ƙa’idojin doka.

By ukarofi

Leave a Reply