
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu na fuskantar halin rashin tabbas a siyasar ƙasar Isra’ila biyo bayan da Shugaba Isaac Herzog ya zaɓi jagoran ‘yan adawa, Gadi Eisenkot a matsayin wanda zai kafa sabuwar gwamnatin ƙasar ta gaba, lamarin da ya ba wa abokin hamayyarsa damar karɓar mulki bayan wani rikitaccen zaɓe da aka gudanar a ƙasar.
Herzegovina ya sanar da wannan matsaya ne a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, 2026 bayan shawarwari da jam’iyyun siyasa da ke wakiltar majalisar dokokin ƙasar mai mambobi 120, wadda aka fi sani da Knesset.
Eisenkot, wanda tsohon shugaban sojin Isra’ila ne kuma shugaban jam’iyyar Yashar, ya samu goyon bayan ‘yan majalisar 67, ciki har da mambobin jam’iyyun Larabawa, yayin da ‘yan majalisa 46 suka zaɓi Netanyahu.
Wannan mataki gagarumar koma-baya ne ga Netanyahu, wanda ɓangarensa na siyasa da addini ya gaza samar masa da wadatattun ƙuri’u na kafa gwamnati bayan babban zaɓen 27 ga Oktoba.
A yanzu, Eisenkot yana da kwanaki 28 na ya tattauna da sauran jam’iyyu kuma ya samu aƙalla kujera 61 na ‘yan majalisar domin samar da mafi rinjaye a Knesset. Zai iya samun ƙarin kwanaki 14 idan yana buƙatar ƙarin lokaci.
Saidai, wannan naɗi ba ya nufin Netanyahu zai sauka a muƙamin firaministan kai-tsaye, yayin da dole ne jagoran adawar ya janyo ra’ayoyin wadatattun jam’iyyu domin su mara masa baya a shirinsa na kafa gwamnatin.
