
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo, ya tunatar da yadda ya koma harkar noma bayan ya yi ritaya daga aikin sojan Nijeriya da yadda matakinsa na dawo wa Nijeriya duk da gargaɗi ya yi sanadiyyar kama shi da tura shi zuwa kurkuku a ƙarƙashin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.
Obasanjo ya kuma bayyana cewa ya yi watsi da tayin mafakar siyasa daga Amurka, duk da cewa wani jakadan Amurka a Nijeriya ya masa gargaɗin cewa za a kama shi muddin ya dawo ƙasar. Haifaffen ɗan Jihar Ogin ɗin kuma ɗaya daga cikin manyan ƙasa, ya bayyana haka ne yayin bayani kan yadda al’amura suka gudana a zamanin mulkin sojin Abacha, a wata hira da BBC New Pidgin ta wallafa a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026.
Biyo bayan kisan Janar Murtala Muhammed, Obasanjo ya zama Shugaban Mulkin Soja a Nijeriya a ranar 13 ga Fabarairun 1976 a lokacin da yake da shekara 38 a duniya. Ya riƙe muƙamin har zuwa 1 ga Oktoba, 1979, a lokacin da ya miƙa mulkin gwamnatin farar hula ta marigayi Shugaba Shehu Shagari.
Ya ce, ya koma aikin noma ne bayan ajiye aikin gwamnati, inda ya ƙara da cewa sana’ar tasa na tafiya yadda ake buƙata har zuwa lokacin da gwamnatin Abacha ta kama shi. Obasanjo, wanda a yanzun yake da shekara 89, ya zargi Abacha da cewa ya yanke hukuncin cewa “wajibi ne ya halaka Obasanjo” kafin ya cimma muradunsa na siyasa.
Ya bayyana cewa, an gargaɗe shi kan kada ya dawo Nijeriya, inda ya ce yana halin tafiya ne a lokacin da wani jakadan Amurka a Nijeriya ya kira shi ya faɗa masa cewa gwamnatin Amurka ta masa tayin samun mafaka a ƙasarta saboda yiwuwar a kama shi idan ya dawo Nijeriya. Ya ce, ya ƙi karɓar tayin ne saboda ya yi imani cewa bai aikata laifin komai ba da zai sa ya guji ƙasarsa.
Bayan ya dawo Nijeriya ne ya ce aka fara da amshe masa fasfo, inda nan ya koma domin cigaba da harkokin nomansa. A nan ne masu gadi suka sanar da shi cewa jami’ai sun zagaye gonar. Ya ce, bayan mintina 15 ne wani ɗan sanda cikin shigar kayan gida ya shaida masa cewa wani sufeto janar na ‘yan sanda (AIG) na son ganinsa domin ya taimaka da bincike akansa.
Duk da cewa bai amsa ba, daga bisani ya kai kansa ofishin ‘yan sandan da a nan AIGn da ya faɗa masa cewa an umarce shi ya kama shi yake aiki. Bayan haka ne, a sa’ilin da ya koma gida, jami’an tsaro suka yi masa dirar mikiya da tsakar dare tare da ɗaukar sa zuwa gidan yari.
