Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Tsohon Janaral Manaja na gidan talabijin na KTTV Alhaji Abba Zayyad ba korar sa aka yi ba shi da kansa ya rubuta takardar ajiye aiki.
A wata wasiƙa da ya rubuta a ranar 2/11/2026 ya sanya hannu zuwa da sakataren gwamnatin Katsina ya buƙaci ajiye aikinsa a ranar 16/11/2026.
A wasikar ya bayyana cewar ya ajiye muƙamin sa don kashin kansa haka kuma yana son cigaba da bibiyar wasu damarmaki.
Zayyad ya gode wa Gwamna Dikko Raɗɗa da ya bashi dama ya bautawa jihar shi har na tsawon shekaru uku.
Yace a shirye yake ya tabbatar da ragamar mulki ga wanda ya gajeshi.
