Rashin sanin muhimmancin rubutu ne ya sa gwamnati bata taka rawa a ciki – Larabi

Spread the love

“Na dakatar da harkar rubutu ne saboda mutuwar kasuwar littattafai”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Da wuya a samu wani wanda ya daɗe yana karance-karancen littattafan Hausa a tsawon shekaru kimanin ashirin da suka gabata, da zai ce bai san wanene marubuci Larabi ba. Sunan da ya zama gama gari a wajen masu karatu da shagunan sayar da littattafai. Cikin lokaci ƙanƙani da bayyanarsa duniyar marubuta da littafinsa mai suna ‘Buwaya’, Larabi ya yi tashin ɗan goma, saboda salon rubutun da ya fito da shi. Sai dai ba da jimawa sosai ba sai aka daina jin ɗuriyar marubucin, sabbin littattafansa suka daina shiga kasuwa, duk kuwa da kasancewar yana nan raye. Sai dai ana ganin gilmawarsa a tsakanin kasuwanci da fagen siyasa. Ko da yake a ýan watannin baya-bayan nan an lura da tsohon marubucin yana ƙoƙarin yin mi’ara koma baya, inda ya sake karkato da tunaninsa kan harkar rubutun adabi, da wani sabon littafin da ya sanya wa suna ‘Gidan Darling’. Wakilin Blueprint Manhaja a Jos, Abba Abubakar Yakubu, ya samu damar zantawa da marubucin, wanda ya bayyana masa dalilin janyewarsa daga fagen rubutu zuwa kasuwanci da siyasa da kuma burinsa a nan gaba.

MANHAJA: Za mu so mu fara da jin wane ne Larabi?

LARABI: To, ni dai asalin sunana Abdullahi Jibril ɗankantoma shine Larabi.

Ko za ka gaya mana tarihinka a taƙaice?

Ni dai haifaffen garin Kano ne. Kuma a nan na yi karatuna dukka na addini da na boko, inda na kai har matakin kammalawa. Na yi karatun ƙaramar Diploma da babba, wato HND a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, inda na karanci ilimin aikin banki da tattalin kuɗi. 

Na yi aiki na taƙaitaccen lokaci a Union Bank. Na kuma yi aiki a Sahad Stores da ke Zoo Road, bayan wani lokaci kuma a shekarar 2011 na bar aiki na koma harkar kasuwanci gadan-gadan. Ina da aure da kuma yara uku.

Yaya aka yi ka samu kanka cikin marubutan adabi?

Na fara rubutu ne a tsakanin 1996 zuwa 1998 tun a lokacin da na fara jin sha’awar ina so na zama marubuci, saboda yadda na kasance mai matuƙar son karance karance na wasu littattafan a baya. Littattafan da na fara rubutawa ban samu damar buga su sun shiga kasuwa ba har yanzu. Saboda ɓacewar da suka yi, abin da ya jawo na rasa ainahin rubutun kuma labarin ya kufce min. Amma dai zan iya tuna sunayen su, ‘Fainusa Da Wanda Yake Ruwa’. A lokacin da fensir na rubuta su a littafin zane-zane na ‘drawing’, har hoton bangon littafin ni na zana a lokacin ban san yadda ake buga littafi ba.

Larabi na daga cikin marubutan da suka yi fice a shekarun baya, menene sirrin ɗaukakar da ka samu?

E, to. Ai ita ɗaukaka daga Allah ne! Idan Allah ya so ɗaukaka bawansa ko ya iya ko bai iya ba sai ya sanya ɗaukakar a tare da shi. Don haka ɗaukakata ba wayona ko dabarata ba ce. Kuma ba don na iya ba. Daga Allah ne! Kuma na gode. Alhamdulillahi. 

Yaya aka yi kuma muka daina ganin littattafanka suna fita?

A gaskiya na dakatar da harkar rubutu ne saboda matsalar da aka samu ta mutuwar kasuwar littattafai. Da kuma canzawar harkokin rayuwa, saboda yadda lokaci yake min ƙarancin. Saboda shi rubutu abu ne da yake buƙatar lokaci da natsuwa.

Littattafai nawa ka wallafa a baya kuma wanne ne bakandamiyarka?

Littattafaina guda sha ɗaya ne da suke kasuwa. Da suka haɗa da ‘Buwaya’, ‘Komai Daɗin Ki Da Miji’, ‘Gudun ƙadara’, ‘Sirrin So’, ‘Maza Tabarmar ƙashi’ da kuma littafin ‘An Yi Ba A Yi Ba’ da wasu ma da ban ambata ba. Sannan akwai wasu guda uku da nake rubutawa a yanar gizo wato ‘Online’, ‘Gidan Darling’, ‘Ja’iba’ da kuma ‘Mace Bututu’, su ma zan buga su in sha Allahu zuwa cikakken littafi su shiga kasuwa. Yanzu dai muna ɗan cin kasuwar su a ‘online’. Bakandamiyata kuwa shine, ‘Komai Daɗin Ki Da Miji’. 

Littafina da ya fara shiga kasuwa shine, ‘Buwaya’, shi ma farko na saka masa sunan ‘Gudummawa Daga Shaiɗan’. Sai wanda zai min aikin littafin ya ce sunan bai hau ba, don za a zaci littafin addini ne ba na adabi ba. Sai na canza masa suna zuwa ‘Buwaya’ ɗin.

Ba ni labarin shi wannan sabon littafin na ka na ‘online’, ‘Gidab Darling’, shi kuma da wanne irin salo ya zo da shi?

Labarin littafin ‘Gidan Darling’ dai har yanzu ban gama rubutawa ba. Ina dai cin kasuwarsa ta ‘Online’. Alhamdulillah ana samun masu siya. Kuma suna nuna yabawa kan salon rubutun. Labarin yana cike da soyayya da nishaɗantarwa da kuma faɗakarwa. Sai an gama labarin mutane za su fahimce shi sosai. Duk da yanzu ma a salon rubutun suna amfana da darussan da ke cikinsa.

Wanne abu ne za ka iya cewa ya faru da kai na farin ciki ko akasin haka ta dalilin rubutun littafi, wanda ba za ka iya mantawa da shi ba?

To, a ɓangaren farin ciki dai shine, wata matar ɗan majalisar tarayya a Jamhuriyar Nijar ta taɓa rubuto min wasiƙa, tana neman don Allah in je in auri wata daga cikin yaranta mata guda biyar. Ban da ita ma akwai wasu mata da yawa a lokacin da ke rubuto min wasiƙa cewar suna so na da aure. Wannan yana sanyawa na yi farin ciki da nishaɗi idan na tuna yadda mata ke tururuwar son na aure su ko na yi abota da su duk saboda rubutuna. 

A ɓangaren baƙin ciki kuwa akwai wadda na taɓa sanya sunanta cikin waɗanda na yi wa godiya ko tukuici sai kuma na sanya sunanta a matsayin jarumar littafin. Labarin ko kaɗan bai yi kama da nata ba. Amma sai ita da wanda za ta aura suka ce za su kai ni kotu wai na rubuta labarinta ba izini. Wannan shine abin baƙin ciki dana taɓa fuskanta a cikin tarihin rubutuna na Hausa.

Wanne buri ka ke da shi nan gaba a harkar rubutun adabi?

Ina da burin na sake sabunta dukkan littattafan da na rubuta a baya. Na cire abubuwan da na ke ganin na yi kuskure a baya wajen rubuta su. Ko ta ɓangaren salon rubutun ko salo da jigon labarin. In sha Allahu ina da wannan burin, Allah kuma ya cika min burina.

Bayan rubutu waɗanne harkokin ne suka fi janye hankali da lokacinka?

Harkar kasuwancina, ita ce mafi muhimmanci da jan lokacina. Ina son kasuwanci sosai. Don ita na karanta ko a makaranta, kuma ta yi min riga da wando har da hankicin goge fuska. (Dariya).

Kwanaki mun ga fostar ka ta fara yawo a zaurukan sada zumunta, ko ka shiga siyasa ne?

ƙwarai na shiga siyasa. Na fito takarar ɗan Majalisar Dokoki ta Jiha a Jam’iyyar PRP Nasara. Amma ban samu damar kaiwa ga matakin yin zaɓen fidda gwani ba, saboda wasu dalilai ya sa na janye. Sai zuwa nan gaba in mu na da yawancin rai da lafiya, in sha Allahu za mu fito da ƙarfin mu a fafata da mu a fagen siyasar Nijeriya.

Wanne irin haɗin gwiwa ka ke ganin ya kamata a samu tsakanin tsofaffin marubuta da matasa masu tasowa don farfaɗo da harkar rubutu a Arewa?

Gaskiya ne, ya kamata a zauna a yi wani taro na gangamin wayar da kai da haɗin kai ga dukkan marubuta, tsofaffi da masu tasowa. Sannan a shirya waɗansu bitoci na salon irin rubutun da zamani yake son tafiya da shi.

Wacce rawa gwamnati da masu hannu da shuni za su iya takawa wajen bunƙasa harkar rubutun adabi?

A Afirka ko na ce a nan Nijeriya ba su da ita, saboda ba su ɗauki harkar rubutu a matsayin sana’a ko wani abu mai muhimmanci ba. Idan ka tunkari gwamnati da maganar rubutun littafi za ta kalleka a matsayin wani marar abin yi ne. Kazalika masu hannu da shunin na mu saɓanin ƙasashen Turai da suke kallon marubuci a matsayin wata babbar kadara da zai iya juya duniya da tsinin alƙalaminsa.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarka?

E, gaskiya suna da yawa. Amma ina amfani da, gudun ƙaddara guzirin tadda ita, a matsayin karin maganar da take da tasiri a wajena.

Mun gode ƙwarai da gaske.

Ni ma na gode.

By ukarofi

Leave a Reply