Za a hukunta waɗanda suka kai wa ayarin APC hari a Katsina – Ɗangiwa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu/Dikko 2027 ta yi alƙawarin cewa waɗanda suka kai hari kan magoya bayanta a lokacin rangadin yaƙin neman zaɓe a shiyyar Sanata ta Funtua za a hukunta su, tare da bayyana cewa ba za ta lamunci tashin hankali na siyasa ba, yayin da take shirin faɗaɗa rangadinta zuwa Shiyyoyin Sanata na Daura da Katsina.

Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓe, Arch. Ahmed Musa Ɗangiwa, ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga manema labarai a hedikwatar majalisar da ke Dandagoro, a Katsina.

Ɗangiwa ya yi Allah-wadai da hare-haren da ake zargin ‘yan daba na siyasa suka kai a Malumfashi da Yankara, yana mai cewa abin da ba a yarda da shi ba ne, kuma barazana ce ga dimokuraɗiyya. Ya nuna ta’aziyyarsa ga waɗanda abin ya shafa, sannan ya sake jaddada aniyar majalisar na gudanar da yaƙin neman zaɓe ba tare da tashin hankali ko tsoratarwa ba.

Ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi wajen binciken lamarin, su kuma tabbatar an kama duk wanda aka samu da laifi a gurfanar da su a gaban kotu, tare da ƙara matakan tsaro don hana sake afkuwar lamarin Ya ce: “majalisar yaƙin neman zaɓe ta yi Allah-wadai da tashin hankalin siyasa, tsoratarwa da lalata dukiya, ba tare da la’akari da waɗanda suka aikata ba. Zaɓe ya kamata ya haɗa kan jama’a, ba ya raba su ko ya jefa rayuka da dukiyoyinsu cikin haɗari ba.”Inji Ahmad Dangiwa.

Yayin da yake yaba wa jami’an tsaro bisa gaggawar da suka yi, Ɗangiwa ya buƙace su da su kammala bincike cikin gaggawa, su kuma tabbatar an yi adalci bisa doka. Haka kuma, ya yi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da ta gaggauta aiwatar da cikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya da ta shafi dukkan jam’iyyun siyasa, domin tabbatar da yaƙin neman zaɓe na lumana kafin babban zaɓen 2027.

Kwamitin ta kuma yi kira ga jam’iyyun adawa da su daidaita jadawalin yaƙin neman zaɓensu, sannan su cire allunan tallan yaƙin neman zaɓe inda ya zama dole, domin rage cunkoso da kuma kauce wa fuskantar juna.

Ɗangiwa ya yaba wa shugabannin APC, magoya baya da ƙungiyoyin manema labarai bisa haɗin kai da rahotanni masu adalci a duk tsawon rangadin yaƙin neman zaɓe wanda ya zagaya dukkan ƙananan hukumomi 11 na Shiyyar Sanata ta Funtua.

Da kammala ɓangaren Funtua, ya sanar da cewa yaƙin neman zaɓen zai koma Shiyyar Sanata ta Daura kafin ya wuce zuwa Shiyyar Sanata ta Katsina, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin isa ga dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar.

Ya bayyana cewa matakan da za su biyo baya za su ƙarfafa nasarorin da aka samu a rangadin Funtua ta hanyar ingantaccen tsari, ƙarfafa kayan aiki, inganta hulɗa da manema labarai da kuma ƙara tuntuɓar jama’a a matakin ƙasa, tare da nuna ayyukan ci gaba na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Malam Dikko Umaru Raɗɗa.

By ukarofi

Leave a Reply