2027: INEC ta cire hotunan AI daga rajistar masu zaɓe

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta cire hotunan da aka ƙirƙira ta amfani da ƙirƙirarriyar fasahar AI, waɗanda aka ɗora a cikin rajistar masu zaɓe ta ƙasa, tare da gano jami’an hukumar da ke da hannu wajen aikata hakan a jihohi 10 domin ɗaukar matakan ladabtarwa a kansu.

Kwamishinan Hukumar INEC na ƙasa, Mohammed Haruna, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin wani taron tattaunawa ta yanar gizo mai taken AI, Yaɗa Labaran ƙarya da Zaɓen Nijeriya na 2027: Kare Gaskiya da Tabbatar da Ingancin ƙuri’a, wanda Gidauniyar Kafafen Yaɗa Labarai ta jaridar PUNCH ta shirya.

Haruna, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Masu Zaɓe na hukumar, ya bayyana cewa lamarin na daga cikin manyan ƙalubalen da INEC ke fuskanta a halin yanzu. Ya ce hukumar na fuskantar matsala wajen hana mutane yin amfani da fasahar zamani wajen gyara, ƙawata ko sauya kamannin hotunansu kafin su ɗora su a cikin rajistar masu zaɓe.

Sai dai kwamishinan ya bayyana cewa hukumar ta gano wasu jami’anta da ke da hannu wajen aikata irin wannan ba daidai ba, kuma ta fara ɗaukar matakan da suka dace domin magance matsalar. A kalamansa, “Mun riga mun gano ɗaya daga cikin ƙalubalen da muke fuskanta, wanda shi ne yadda aka ɗora hotuna da dama da aka ƙirƙira ta amfani da fasahar AI a cikin rajistar masu zaɓe. Kamar yadda muka bayyana a baya, mun riga mun cire waɗannan hotuna.”

Haruna ya yi bayanin cewa duk da cewa yana da wahala hukumar ta hana jama’a amfani da fasahar zamani wajen sauya hotunansu kafin ɗora su a rajistar masu zaɓe, amma tana da cikakken iko wajen ɗaukar mataki kan irin wannan laifi idan jami’anta ne suka aikata shi. Ya ce, “Amma idan jami’anmu ne suka aikata hakan, wannan abu ne da yake ƙarƙashin ikonmu. Muna kan aiwatar da matakan da suka dace domin magance matsalar. An riga an gano tare da yi wa waɗannan jami’ai alama ta musamman domin ɗaukar mataki a kansu.”

Kwamishinan ya bayyana cewa an gano jami’an da abin ya shafa a kusan jihohi 10, kuma za su fuskanci matakan ladabtarwa bisa dokokin aikin hukumar. Ya ƙara da cewa, “Muna da sunayensu a kusan jihohi 10, kuma a bayyane yake cewa za su fuskanci matakan ladabtarwa.”

Yayin da yake magana kan shirye-shiryen hukumar na tsara yadda za a yi amfani da fasahar basirar wucin gadi a harkokin zaɓe, Haruna ya ce INEC ta riga ta samar da wata manufar amfani da wannan fasaha, amma har yanzu tana kan aikin kammala tsara ta yadda za a fara aiwatar da ita.

Ya bayyana cewa fasahar AI na haifar da sabbin ƙalubale da ke ci gaba da sauyawa, lamarin da ya sa hatta ƙasashen da suka ci gaba a fannin dimokuraɗiyya ke fuskantar wahala wajen samar da cikakkun dokoki da ƙa’idojin da za su kula da amfani da ita. A cewarsa, “Kamar yadda kuka sani, wannan sabon fage ne da ake ci gaba da gano abubuwa a cikinsa. Hatta ƙasashen da suka fi ci gaba ba su da cikakkun manufofi da ƙa’idoji na musamman kan AI, saboda fasahar na ci gaba da sauyawa da bunƙasa.”

By ukarofi

Leave a Reply