Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ’yan kasuwar kayan marmari da ke babbar kasuwar Zuba, a Babban Birnin Tarayya Abuja, sun nuna damuwarsu kan mummunar lalacewar hanyar shiga kasuwar, inda suka ce matsalar na kawo cikas ga harkokin kasuwanci, hana kwastomomi zuwa kasuwar tare da ƙara musu kuɗin sufuri.
’Yan kasuwar sun bayyana hakan ne yayin tattaunawa daban-daban da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya yi da su a ranar Laraba a Abuja. Sun ce hanyar ta daɗe tana lalacewa, amma matsalar ta fi ƙamari a lokacin damina, inda manyan ramuka, taɓo da kuma rashin ingantaccen magudanar ruwa ke sa hanyar kusan zama ba a iya wucewa. A cewarsu, lalacewar hanyar na hana kwastomomi zuwa kasuwar yadda ya kamata, tare da kawo tsaiko wajen jigilar ’ya’yan itatuwa da kayan lambu daga gonaki zuwa kasuwar.
Wani dillalin ’ya’yan itatuwa, Mohammed Usman, ya ce da dama daga cikin direbobin motocin haya da na kasuwanci sun daina amfani da hanyar saboda lalacewarta, lamarin da ke tilasta wa ’yan kasuwa biyan kuɗin sufuri fiye da yadda ya kamata. Ya ce, “Lalacewar wannan hanya ta yi matuƙar shafar harkokin kasuwancinmu. Da dama daga cikin masu jigilar kaya suna ƙara kuɗin mota saboda fargabar lalacewar motocinsu. Wasu kwastomomi ma idan suka ga irin halin da hanyar take ciki sai su juya su koma, yayin da wasu ke fifita zuwa kasuwannin da hanyoyinsu suka fi sauƙin bi.”
Shi ma wani ɗan kasuwa, Augustine Igwe, ya ce motocin da ke ɗauko ’ya’yan itatuwa daga gonaki kan samu matsalar lalacewa a hanya akai-akai saboda munin hanyar. Ya ce, “Muna kashe kuɗi masu yawa wajen gyaran motocinmu, baya ga biyan kuɗin sufuri mai tsada. A ƙarshe, waɗannan ƙarin kuɗaɗe suna jawo tashin farashin ’ya’yan itatuwa. Wani lokaci motocin da ke ɗauke da ’ya’yan itatuwa kan maƙale a hanya, lamarin da ke jawo tsaiko da lalacewar wasu kayayyaki. Daga ƙarshe, masu saye ne ke ɗaukar nauyin waɗannan ƙarin kuɗaɗe.”
Wata kwastoma, Esther Okoli, ta bayyana hanyar a matsayin babbar matsala, musamman ga tsofaffi da kuma iyayen da ke zuwa kasuwar tare da ƙananan yara. Ta ce, “Hanyar tana cikin mummunan hali. Da yawa daga cikin kwastomomi suna ƙorafi tun kafin su zo kasuwar, yayin da masu motocin haya ke ƙara mana kuɗin mota saboda lalacewar hanyar. Da zarar an yi ruwan sama, hanyar kan zama kusan ba za a iya wucewa ta cikinta ba saboda taruwar ruwa da kuma manyan ramukan da ke cikinta. Jigilar kaya a irin wannan yanayi na da matuƙar wahala.”
Wani mai sayayya a kasuwar, Emmanuel Johnson, ya ce lalacewar hanyar na ƙara tsadar kuɗi da wahalar jigilar kayayyakin da aka saya daga kasuwar. Ya ce, “Ina zuwa wannan kasuwa ne saboda arahar kayayyaki, amma lalacewar hanyar na sanyaya wa masu sayayya gwiwa. Motocin haya da dama suna ƙin zuwa cikin kasuwar, lamarin da ke tilasta mana ɗaukar kayan da muka saya na dogon zango.”
Shi ma wani direban motar haya, Abdullahi Ibrahim, ya ce yawan amfani da hanyar na ƙara kuɗin kula da motocinsu, sakamakon lalacewar tayoyi da sassan dakatar da motsin mota. Saboda haka, ya yi kira ga Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya Abuja da ta mayar da gyaran hanyar cikin muhimman ayyukan da ya kamata ta ba fifiko, domin sauƙaƙa zirga-zirga da kuma tallafa wa ’yan kasuwar da ke gudanar da harkokinsu a yankin.
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) ya rawaito cewa kasuwar ’ya’yan itatuwa ta Zuba na samar da ’ya’yan itatuwa da kayan lambu a kullum, inda dubban masu sayayya daga cikin Abuja da sauran al’ummomin da ke maƙwabtaka da ita ke dogaro da kasuwar. ’Yan kasuwar da masu sayayya sun bayyana fatan cewa ɗaukar matakin gaggawa daga gwamnati zai inganta hanyar shiga kasuwar, rage kuɗin sufuri tare da bunƙasa harkokin tattalin arziki a yankin.
