Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Alƙalin-Alƙalai na Nijeriya (CJN), Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta rantsar da sabbin mambobin Kotunan ɗaukaka ƙarar Zaɓe da aka naɗa gabanin babban zaɓen 2027, inda ta buƙace su da su kare mutuncin bangaren shari’a tare da gudanar da adalci ba tare da tsoro ko nuna son kai ba.
Rahoton News Point Nigeria ya ce an gudanar da bikin rantsarwar ne a zauren Body of Benchers da ke Abuja. Taron ya kuma yi daidai da ƙaddamar da sabon bugu na biyu na Littafin Jagorar Shari’ar Zaɓe (Judicial Electoral Manual), tare da wani taron horaswa na musamman ga jami’an shari’a.
A jawabinta, Mai Shari’a Kekere-Ekun ta buƙaci alkalan kotunan zaɓen da su kasance masu bin rantsuwar da suka yi, su guji katsalandan daga ’yan siyasa da sauran ɓangarori, tare da kiyaye bin doka da oda yayin da ƙasar ke shirin gudanar da wani babban zaɓe.
Ta bayyana cewa zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta ƙasa zai gudana ne a ranar 16 ga Janairun 2027, yayin da zaɓen gwamnoni da na majalisun dokokin jihohi zai gudana a ranar 6 ga Fabrairun 2027.
Ta tunatar da sabbin mambobin kotunan zaɓen cewa kundin tsarin mulki da dokokin ƙasa sun tanadi ƙayyadaddun lokuta na sauraron ƙararrakin zaɓe, don haka babu damar yin jinkiri ba tare da dalili ba, tsawaita shari’a ko rashin kyakkyawan tsarin tafiyar da shari’o’i.
Alƙalin-Alƙalai ta kuma yi gargaɗi ga lauyoyi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin yaɗa labarai da sauran jama’a kan guje wa ayyukan da ba su dace ba, ciki har da amfani da shari’ar gaggawa ta eɗ parte ta hanyar da ba ta dace ba, da kuma yaƙin neman goyon baya a kafafen sada zumunta domin rinjayar tunanin jama’a kan shari’o’i ko tsoratar da alkalan da ke sauraron su.
Ta jaddada cewa kare dimokuraɗiyya alhakin kowa ne, don haka INEC, hukumomin tsaro da masu aikin lauya dole ne su sauke nauyin da doka ta ɗora musu yadda ya kamata.
Sai dai ta bayyana cewa aikin bangaren shari’a shi ne warware rikice-rikicen zaɓe bisa doka da kuma hujjojin da aka gabatar a gaban kotu.
A wani ɓangare kuma, INEC ta sake jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gudanar da zaɓe da bangaren shari’a domin tabbatar da sahihin zaɓe da kuma warware rikice-rikicen zaɓe yadda ya kamata.
Da yake jawabi a wani taron horaswa na kwanaki uku ga alkalai da mambobin kotunan zaɓe a Abuja, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, wanda ya halarci taron, ya bayyana kotunan ƙararrakin zaɓe a matsayin muhimman hanyoyin da kundin tsarin mulki ya tanada domin warware saɓanin da ya taso daga zaɓe, rage rikicin siyasa da kuma ƙarfafa amincewar jama’a ga bin doka da oda.
Yayin da yake magana kan ƙarin sarkakiyar shari’o’in zaɓe, Amupitan ya nuna cewa haɗuwar fasahar zamani da sabbin barazanar da ake samu a duniyar dijital na daga cikin muhimman abubuwan da ya kamata a kula da su gabanin zaɓen 2027.
Ya ce fasahohin da ake amfani da su wajen zaɓe, ciki har da na’urar tantance masu zaɓe ta BɓAS da kuma shafin duba sakamakon zaɓe na INEC mai suna IReɓ, sun taimaka wajen ƙara gaskiya da bayyana gaskiyar tsarin zaɓe.
Sai dai ya jaddada cewa bangaren shari’a ma yana buƙatar shiri domin fuskantar sabbin ƙalubalen fasaha, ciki har da hotunan bidiyo da sauti na bogi da ake ƙirƙira ta amfani da fasahar AI (deepfakes), da sauran bayanan ƙarya da ake yaɗawa a intanet waɗanda ka iya rage amincewar jama’a da kuma barazana ga sahihancin zaɓe.
