Hukumar bogi: Gwamnatin Tarayya ta shigar da sabbin tuhume-tuhume 36 kan Adeniyi

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta shigar da sabuwar takardar tuhuma mai ƙunshi tuhume-tuhume 36 da aka yi wa kwaskwarima a kan Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta ƙasashen Waje ta Fadar Shugaban ƙasa (PFIPC), Adeyemi Adeniyi, da wasu mutane huɗu, bisa zargin ƙirƙirar takardun bogi, bayar da bayanan ƙarya da damfara.

Rahoton Blueprint ya ce Adeniyi ya gurfana tare da waɗanda ake tuhuma tare da shi a gaban Mai Shari’a Halilu Yusuf na Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya da ke Maitama, Abuja, ranar Litinin.

Sai dai ba a samu damar fara karanta sabbin tuhume-tuhumen ga waɗanda ake tuhuma ba, sakamakon rashin halartar mutum na huɗu, Florence Omemah, wadda aka ce ba ta da lafiya.

A yayin zaman kotun, lauyan masu gabatar da ƙara, Sylvanus Tahir, ya sanar da kotu cewa Omemah tana karɓar magani a wani asibiti da ke Abuja. Daga nan ya nemi a ɗage shari’ar na tsawon kwanaki bakwai domin ta samu sauƙi ta halarci kotu domin amsa tuhumar da ake mata.

Sai dai lauyan Adeniyi, Ibrahim Angulu, ya buƙaci kotun da ta ɗage shari’ar na ɗan gajeren lokaci domin ya samu damar neman belin wanda yake karewa. Ya kuma shaida wa kotu cewa Adeniyi ya shafe sama da kwanaki 200 a tsare.

A wani ɗan gajeren hukunci, Mai Shari’a Yusuf ya ɗage shari’ar zuwa ranar 18 ga Nuwamba domin gurfanar da dukkan waɗanda ake tuhuma.

Alƙalin ya kuma bayar da umarnin a ci gaba da tsare Adeniyi a gidan gyaran hali na Kuje, yayin da sauran waɗanda ake tuhuma za su ci gaba da kasancewa a hannun Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaƙa da Hakan (ICPC).

Shari’ar ta samo asali ne daga zargin cewa Adeniyi ya kafa wata hukumar gwamnatin tarayya da babu ita, mai suna Presidential Foreign Investment Promotion Council, sannan ya riƙa gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar.

Masu bincike sun yi zargin cewa hukumar ba ta da wata hujjar doka da ta ba ta damar wanzuwa, kuma Adeniyi ya ƙirƙiri takardun naɗin aiki da sa hannun da aka danganta da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa domin halatta matsayin da yake ikirarin yana da shi.

A cewar masu binciken, ya mamaye ofisoshin da a baya Hukumar Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tattalin Arziki (Presidential Economic Advisory Council) take amfani da su a Sakatariyar Tarayya da ke Abuja, sannan ana zargin ya gudanar da tarurruka ba bisa ƙa’ida ba da wasu jakadun ƙasashen waje.

An kuma zarge shi da neman takardun izinin shiga Amurka ta hanyar da ba ta dace ba, tare da gudanar da asusun banki guda 34.

Masu binciken sun ƙara da zargin cewa ya yi amfani da giɓin da ke cikin tsarin ma’aikatan gwamnati wajen neman a ware wa hukumar da ake zargin ƙirƙirarta aka yi Naira biliyan 1.302 a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Bayan gabatar da wani rahoton wucin gadi ga Shugaba Bola Tinubu, an ruwaito cewa ICPC ta gano wasu hukumomi biyu da ake zargin ƙirƙirarsu aka yi kuma suna da alaƙa da Adeniyi. Su ne Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta FCT da Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta ƙasashen Waje.

Hukumar ta kuma ba da shawarar ɗaukar matakan ladabtarwa kan wasu jami’an gwamnati da ake zargin sun taimaka wajen aiwatar da wannan shiri.

A watan Oktoban 2026, Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da tuhumar farko mai ƙunshi tuhume-tuhume takwas, bayan da aka samu matsala kan ikon kotun na sauraron shari’ar, lamarin da ya sa Antoni Janar na Tarayya ya janye ƙarar.

Daga bisani ICPC ta shigar da sabuwar takardar tuhuma mai ƙunshi tuhume-tuhume 36, tare da ƙara wasu waɗanda ake zargi da hannu a lamarin.

Adeniyi ya musanta zarge-zargen damfara, ƙirƙirar takardun bogi da kuma yin kamar wani jami’i ne da ba shi ba. Har yanzu yana tsare a gidan gyaran hali na Kuje yayin da shari’ar ke ci gaba.

By ukarofi

Leave a Reply