Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani rahoton bincike ya bayyana cewa shirin Shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu na bunƙasa amfani da iskar gas ɗin CNG a matsayin madadin man fetur na fuskantar babban koma-baya, duk da cewa akwai asusun kuɗi da ya haura Naira tiriliyan uku da aka ware domin gina muhimman cibiyoyin samar da iskar gas ɗin a faɗin Nijeriya.
Rahoton ya ce, yayin da kuɗaɗen ke ci gaba da kasancewa ba a amfani da su, direbobi a sassa daban-daban na ƙasar na shafe kwanaki a gidajen mai suna jiran samun iskar gas domin cika tankunan motocinsu. Asusun da ake magana a kai shi ne Asusun Samar da Kayayyakin More Rayuwa na ɓangaren Iskar Gas (MDGIF), wanda aka kafa ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur, tare da miƙa kulawarsa ga Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur (NMDPRA).
An kafa asusun ne domin samar da kuɗaɗen gina manyan cibiyoyin samar da iskar gas da ƙananan cibiyoyin rarraba ta a faɗin Nijeriya. Sai dai bayan shafe shekaru biyu da kafa tsarin, rahoton ya ce babu ko sisi daga cikin kuɗaɗen da aka bai wa kamfanoni 23 da suka cika sharuɗɗan cancanta domin gina waɗannan cibiyoyi.
Wani bincike da kafar InsideBusinessNg ta gudanar ya nuna cewa tawagar gudanarwar asusun, ƙarƙashin jagorancin Babban Daraktan Zartarwa, Wole Adama, ta ƙi sakin sama da Naira tiriliyan uku domin gudanar da ayyukan da aka tsara. Rahoton ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin shugabannin asusun na yawan tafiye-tafiyen ƙasashen waje, waɗanda masu suka ke ganin ba sa samar da wani amfani na zahiri ga shirin.
Sakamakon wannan matsala shi ne ƙarancin iskar gas a gidajen mai da dama a faɗin ƙasar. Daga gidajen mai na Shafa zuwa NIPCO, Mobil da NNPC da ke kan hanyar filin jirgin saman Abuja, da kuma Prince and Princess, Gaduwa, New Nyanya da Zone 1, rahoton ya ce direbobi na fuskantar dogayen layuka, fushi da kuma rufe famfunan iskar gas saboda rashin wadatar kayayyakin. Direbobin da suka gaggauta sauya motocinsu domin amfani da CNG bayan cire tallafin man fetur sun fara nadamar matakin da suka ɗauka.
Wani direban kamfanin jigilar fasinjoji na Bolt, Chukwuma Nnadi, ya ce a wasu lokutan suna shafe sa’o’i bakwai zuwa takwas a layi, amma daga ƙarshe sai a sanar da su cewa iskar gas ta ƙare. Ya ce, a wani lokaci ma ya shafe sa’o’i 26 yana jira ba tare da ya samu damar sayen iskar gas cin ba. Nnadi ya bayyana cewa ba abin fahimta ba ne gwamnati ta ƙarfafa jama’a su koma amfani da CNG, alhali kuwa ba a samar da isasshiyar hanyar samun ta cikin sauƙi da tabbas.
Shi ma wani direban mota mai zaman kansa, Sola Adeoti, ya ce dogayen layukan sun zama ruwan dare a gidajen mai. Ya bayyana cewa ya kwana a gidan mai a ranar da ta gabata, inda ya shafe sa’o’i takwas kafin ya samu iskar gas ɗin da bai kai ya wadatar da motarsa na yini ɗaya ba. Ya ce wannan hali ya zama wata wahala da yake fuskanta a kullum.
A nasa ɓangaren, Hassan Abubakar ya ce matsalar ta janyo masa babban tashin hankali, har ta kai ga rasa damar kasancewa tare da matarsa lokacin da take haihuwa. Abubakar ya bayyana cewa ya shafe kwanaki uku a gidan mai yana jiran samun iskar gas, lamarin da ya sa maƙwabtansa suka garzaya da matarsa asibiti lokacin da naƙuda ta kama ta.
Rahoton ya ce an tsara shirin CNG ne domin rage wa ‘yan Nijeriya raɗaɗin tsadar man fetur, wanda farashinsa ya haura naira 900 kan kowace lita bayan cire tallafi, kuma rikicin da ke tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran ya ƙara tsananta matsin lambar da ake fuskanta a kasuwar makamashi. Sai dai maimakon shirin ya sauƙaƙa wa jama’a, rahoton ya ce ya zama wata sabuwar matsala, inda direbobi ke ɓata sa’o’i masu yawa a layuka, rasa kuɗaɗen shiga da kuma fuskantar ƙarin wahalhalu.
Wani jami’i a cikin Asusun MDGIF, wanda bai bayyana sunansa ba, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake tafiyar da asusun. Ya ce dokar da ta kafa asusun ta tanadi gudanar da aƙalla tarukan kwamitin gudanarwa huɗu a kowace shekara, amma har zuwa lokacin da shekarar ke daf da ƙarewa, taro ɗaya ne kawai aka gudanar. Jami’in ya zargi shugabannin asusun da ɗaukar matakan da ke ƙara tsananta halin ƙunci da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman a wannan shekarar da ake shirin gudanar da zaɓe.
Rahoton ya kuma ce ƙoƙarin jin ta bakin Wole Adama domin ya yi ƙarin bayani kan dalilin da ya sa aka kasa sakin kuɗaɗen da suka haura naira tiriliyan uku, alhali jama’a na fama da matsalar ƙarancin iskar gas, bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala rahoton.
A watan Mayu, Adama ya bayyana cewa asusun MDGIF ya ware naira biliyan 430 domin ayyukan samar da kayayyakin more rayuwa na CNG, yayin ƙaddamar da babbar cibiyar samar da iskar gas ta Rolling Energy, wanda Shugaba Tinubu ya halarta. Sai dai a watan Nuwamba na 2025, ita kanta Hukumar Kula da Albarkatun Man Fetur (NMDPRA) ta bayyana cewa adadin kuɗaɗen da aka ware ya kai Naira biliyan 287.
Wannan bambanci ya jawo tambayoyi kan ainihin inda sauran kuɗaɗen suke, da kuma dalilin da ya sa aka kasa amfani da asusun Naira tiriliyan uku wajen cimma manufar da aka kafa shi dominta. Rahoton ya kammala da cewa ga miliyoyin mutanen da suka sauya motocinsu domin amfani da CNG, gidajen mai sun koma tamkar wuraren kwana, yayin da shirin sauya fasalin makamashi na Shugaba Tinubu ke ci gaba da fuskantar matsalar rashin wadataccen iskar gas.
