Rikicin iyaka a Ethiopia ya tilasta wa dubban mutane tserewa zuwa Kenya

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen cikin gida na daga cikin manyan abubuwan da ke tilasta wa mutane barin gidajensu ba tare da shirin hakan ba, musamman idan rayukansu suka shiga cikin haɗari.

Wani sabon rikici da ya ɓarke a yankin iyakar Ethiopia da Kenya ya tilasta wa dubban mutane tserewa daga muhallansu domin neman mafaka a ƙasar Kenya.

Rahoton Al Jazeera, ya bayyana cewa kimanin mutane 50,000 sun isa yankin Moyale na ƙasar Kenya bayan tserewa daga faɗace-faɗacen da suka ɓarke a yankin Borana da wasu sassan Ethiopia.

Rahoton ya bayyana cewa waɗanda suka tsere sun bar gidajensu ne sakamakon ƙara tsanantar faɗace-faɗace a yankunansu, inda da dama suka isa Kenya ba tare da isassun kayayyakin rayuwa ba.

Wani bincike da hukumar kula da ƙaura ta duniya (IOM) da wasu ƙungiyoyin agaji suka gudanar ya nuna cewa kashi 71 cikin 100 na gidajen da aka bincika ba su da isasshen abinci.

Haka kuma, kashi 80 cikin 100 na mutanen da aka bincika sun bayyana cewa abinci shi ne babban abin da suka fi buƙata.

Matsalar ta haɗa da ƙarancin matsuguni, rashin isasshen ruwan sha da kuma ƙarancin samun kulawar lafiya.

Masu aikin agaji sun bayyana damuwa kan yadda wannan sabon kwararar ‘yan gudun hijira ke ƙara matsin lamba ga al’ummomin da ke zaune a yankin Moyale.

By ukarofi

Leave a Reply