Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
A tarihin Nijeriya akwai wasu tsofaffin garuruwa da birane waɗanda a da suka kasance cibiyoyin mulki, kasuwanci, al’adu da addini, amma a yau sun zama kufai ko kuma wuraren tarihi da ke tunatar da al’umma irin ɗaukakar da suka taɓa yi.
Wasu daga cikin waɗannan garuruwa sun kasance manyan cibiyoyin dauloli masu ƙarfi, inda sarakuna ke gudanar da mulki, ’yan kasuwa ke gudanar da harkokinsu, sannan masana da masu fasaha ke bunƙasa ilimi da al’adun al’ummominsu.
Sai dai abubuwa da dama, ciki har da yaƙe-yaƙe, rikice-rikicen siyasa, sauyin yanayin tsaro, matsalolin muhalli da kuma sauye-sauyen tsarin mulki, sun haddasa durƙushewar wasu daga cikinsu, har ma mazaunansu suka yi hijira zuwa wasu wurare.
Yana da muhimmanci a fahimci cewa ba duk garuruwan da ake kira sun ɓace ne suka gushe gaba ɗaya ba. Wasu an bar su ne a matsayin wuraren zama, amma har yanzu ana iya ganin ragowar gine-ginensu, tsoffin katangunsu da sauran alamomin tarihi.
Ga wasu daga cikin fitattun tsofaffin garuruwa da matsugunan tarihi a Nijeriya waɗanda suka shiga wannan hali.
1. Oyo-Ile: Tsohon babban birnin daular Oyo
Oyo-Ile, wanda aka fi sani da Old Oyo, yana daga cikin manyan tsofaffin biranen da suka taka muhimmiyar rawa a tarihin Yarbawa da ma Afirka ta Yamma baki ɗaya.
Birnin shi ne cibiyar mulkin daular Oyo, wadda ta kasance ɗaya daga cikin manyan daulolin da suka yi fice wajen ƙarfin soja, kasuwanci da tsarin shugabanci a yankin.
A tsawon ƙarnuka, Oyo-Ile ya bunƙasa sosai, inda ya zama cibiyar tattalin arziki da siyasa. Ana kuma ganin cewa birnin ya taɓa kasancewa mai yawan jama’a, musamman a ƙarni na 18.
Sai dai a ƙarni na 19, rikice-rikicen siyasa da yaƙe-yaƙe suka fara raunana daular. Mamayar da mayaƙan Fulani suka yi wa yankin da kuma faɗaɗar rikicin da ya shafi Ilorin sun taimaka wajen kawo ƙarshen zaman lafiya a birnin.
A shekarar 1837 ne aka bar tsohon birnin gaba ɗaya, inda mazaunansa suka ƙaura zuwa kudu, suka kafa sabon birnin Oyo, wanda yake da nisan kusan kilomita 130 daga tsohon wurin.
A yau, ragowar tsohon Oyo na cikin wuraren tarihi da ake kula da su a matsayin gandun dajin ƙasa na Old Oyo.
2. Birnin Ngazargamu: Tsohon cibiyar daular Kanem-Borno:
Ngazargamu, wanda aka fi sani da Birnin Ngazargamu, yana cikin jihar Yobe ta yanzu. Ya kasance ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin mulkin daular Kanem-Borno.
An kafa birnin a ƙarni na 15 a zamanin Mai Ali Gaji, wanda ya kasance ɗaya daga cikin sarakunan da suka taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa daular Borno.
Birnin ya zama cibiyar siyasa, tattalin arziki da harkokin soja na daular, inda sarakuna da manyan jami’an gwamnati ke gudanar da mulki. Haka kuma, kasancewarsa kusa da muhimman hanyoyin kasuwanci ya taimaka wajen bunƙasar sa.
Tsawon fiye da ƙarni uku, Ngazargamu ya kasance babban birnin daular Kanem-Borno, har zuwa farkon ƙarni na 19.
A shekarar 1808, mayaƙan jihadin Fulani suka kai hari kan birnin, suka mamaye shi tare da lalata shi, lamarin da ya tilasta wa mazaunansa barin wurin.
Wannan lamari ya kawo ƙarshen ɗaukakar birnin a matsayin cibiyar mulki, duk da cewa tarihin daular Borno ya ci gaba a wasu wurare.
3. Oke-Idanre: Tsohon garin da aka gina a saman duwatsu:
Oke-Idanre, wanda ke cikin jihar Ondo, wani tsohon gari ne da aka gina a saman manyan duwatsu, inda al’ummar Idanre suka zauna tsawon ƙarnuka da dama.
An zaɓi wannan wuri ne saboda yanayin duwatsunsa da ya samar da kariya daga hare-haren maƙiya. A wancan lokaci, zama a saman tsaunuka wata muhimmiyar hanya ce ta kare al’umma daga hare-haren mayaƙa da masu fashin daji.
A cikin tsohon garin akwai fadar sarki, wuraren ibada na gargajiya, kotun gargajiya da sauran gine-gine da ke nuna irin tsarin rayuwar mutanen zamanin.
Sai dai yayin da yanayin tsaro ya fara inganta, tare da buƙatar samun ƙarin fili don noma, gine-gine da sauran abubuwan more rayuwa, mazauna garin suka fara tunanin saukowa daga kan tsaunukan.
A shekarar 1923 ne aka fara aiwatar da sauyin matsugunin, inda daga baya, zuwa shekarar 1934, yawancin al’ummar suka koma sabon garin Odode-Idanre da ke ƙasan duwatsun.
Duk da cewa an bar tsohon garin, bai rasa muhimmancinsa ba, domin har yanzu ana gudanar da wasu bukukuwa da al’adun gargajiya a wurin.
A yau, Oke-Idanre na daga cikin muhimman wuraren tarihi da al’adu a Nijeriya, kuma yana cikin jerin wuraren da Nijeriya ta gabatar wa UNESCO domin a yi la’akari da sanya su cikin wuraren tarihi na duniya.
4. Tsoffin matsugunan al’ummar Nok: Sirrin wata tsohuwar wayewa
Wayewar al’ummar Nok na daga cikin tsofaffin wayewar da aka taɓa samu a Afirka ta Yamma. Wannan al’umma ta rayu ne a yankin tsakiyar Nijeriya, musamman a sassan jihar Kaduna da kewaye.
Binciken masana tarihi da masu binciken kayan tarihi ya nuna cewa al’ummar Nok sun rayu tun kimanin shekara ta 1500 kafin haihuwar Annabi Isa, har zuwa kusan farkon ƙarni na farko bayan haihuwarsa, duk da cewa tsawon lokacin ya bambanta bisa ga rabe-raben binciken masana.
Al’ummar sun shahara wajen ƙera mutum-mutumin yumɓu masu fasaha ta musamman, waɗanda aka fi sani da Nok Terracotta. Haka kuma, sun kasance cikin al’ummomin farko da suka bunƙasa aikin narkar da ƙarfe a wannan yanki.
Binciken da aka gudanar a Taruga da sauran wurare ya nuna cewa sun kasance manoma, masu kiwon dabbobi da kuma ƙwararrun masu sana’o’i.
Sai dai abin mamaki shi ne yadda wannan wayewa ta ragu, har aka daina samun alamomin fasaharta a wuraren binciken tarihi. Har yanzu masana ba su tabbatar da ainihin dalilin da ya haddasa ƙarshen wannan wayewa ba.
Wasu masana sun yi hasashen cewa lalacewar muhalli, yawan amfani da albarkatun ƙasa da sauye-sauyen tattalin arziki na iya kasancewa cikin abubuwan da suka taimaka wajen durƙushewar al’ummar.
Duk da haka, ba a tabbatar da cewa dukkan al’ummar sun ɓace ko sun mutu ba. Abin da aka tabbatar shi ne cewa tsohon tsarin rayuwarsu da alamomin fasaharsu sun daina bayyana kamar yadda suke a baya.
5. Isale: Tsohon matsugunin da ya ɓace a Abeokuta
Isale wani tsohon matsuguni ne da ke yankin kudu maso gabashin Abeokuta, a jihar Ogun.
Wannan gari ya kasance wurin zama na wata al’umma a zamanin da, amma daga baya mazaunansa suka bar shi, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin wuraren da masana tarihi ke nazari domin gano irin rayuwar mutanen da suka zauna a cikinsa.
Binciken kayan tarihi da aka gudanar a wurin ya gano wasu kayayyaki da suka haɗa da kuɗin kwark, kayayyakin ƙarfe, ƙasusuwan dabbobi da kuma bututun shan taba.
Waɗannan abubuwan da aka gano sun taimaka wajen fahimtar yadda mutanen da suka zauna a garin suke gudanar da rayuwarsu, da irin sana’o’insu da hulɗar kasuwanci.
Duk da cewa ba a da cikakken bayani kan dukkan dalilan da suka sa aka bar garin, binciken ya nuna cewa wurin na ɗauke da muhimman bayanai game da tarihin al’ummar yankin Abeokuta.
6. Okeiho da Igbetti: Garuruwan da aka ƙaura daga saman tsaunuka
Okeiho da Igbetti na daga cikin garuruwan Yarbawa da suka taɓa kasancewa a wuraren da ke saman tsaunuka, kafin mazaunansu su koma ƙananan filayen da suka fi dacewa da zaman rayuwa.
A zamanin da, al’ummomi da dama sun zaɓi zama a kan tsaunuka ne saboda kariya daga hare-haren maƙiya. Amma yayin da yanayin tsaro ya sauya, tare da shigowar mulkin mallaka da sauye-sauyen tsarin gudanar da al’umma, wasu daga cikinsu suka fara sauya matsugunansu.
Binciken wani masani mai suna Michael B. Gleaɓe, wanda aka wallafa a mujallar Africa a shekarar 1963, ya bayyana cewa an ƙaura da garin Igbetti zuwa sabon wuri a shekarar 1905, yayin da aka ƙaura da Okeiho a shekarar 1917.
Wannan sauyi ya nuna yadda abubuwan da suka shafi tsaro, mulki da sauƙin rayuwa suka taimaka wajen sauya tsarin matsugunan al’ummomin gargajiya a yankin Yarbawa.
Duk da cewa waɗannan garuruwa ba su ɓace gaba ɗaya ba, tsoffin matsugunansu na kan tsaunuka sun kasance wani muhimmin ɓangare na tarihin yankin.
Me ya haddasa ɓacewar waɗannan garuruwa?
Idan aka yi nazari kan tarihin waɗannan tsofaffin garuruwa, za a fahimci cewa ba wani abu guda ne ya haddasa barinsu ko durƙushewarsu ba. Akwai dalilai daban-daban da suka taka rawa, waɗanda suka haɗa da:
1. Yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen siyasa: Hare-haren mayaƙa, rikicin sarauta da fadace-faɗace tsakanin dauloli sun tilasta wa wasu al’ummomi barin matsugunansu.
2. Sauyin yanayin tsaro: Wasu al’ummomi sun bar wuraren da suke zaune a kan tsaunuka bayan da zaman lafiya ya samu, suka koma filayen da suka fi sauƙin gudanar da rayuwa.
3. Matsalolin muhalli: Sauyin yanayi, ƙarancin albarkatun ƙasa da matsalolin samar da abinci na iya zama sanadin durƙushewar wasu tsoffin matsuguna.
4. Sauyin tsarin mulki: Rushewar dauloli da sauyin cibiyoyin mulki sun sa wasu tsoffin birane rasa matsayinsu na cibiyoyin gudanarwa.
5. Bunƙasar sababbin birane: Wasu al’ummomi sun ƙaura ne zuwa sababbin wurare domin samun filayen noma, kasuwanci da sauran abubuwan more rayuwa.
A ƙarshe, duk da cewa wasu garuruwa sun rasa mazaunansu, tarihin da suka bari ba zai taɓa gushewa ba matuƙar ana ci gaba da bincike da adana shi.
Madogara
An gina wannan rubutu ne bisa bayanan binciken tarihi, nazarin kayan tarihi da wallafe-wallafen masana.
