
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Yanki da ke zaune a Gundumar Gudu ta Abuja, ta sanar da ɗage shari’ar neman saki da ya haɗa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da matarsa da suka rabu, Zainab Rabi’u Musa Kwankwaso, zuwa ranar 15 ga Disamba, 2026 domin sauraro. An gabatar da shari’ar ne a ranar Talata, 17 ga Nuwamba biyo bayan aiken takardar gayyata mai lamba CV/97/26 da ta umarci gwamnan ya je gaban kotun a ranar.
A lokacin da aka bayar da damar yin shari’a kan ƙarar, wakilin gwamnan kuma kwamishinan yaɗa labaran Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya shaida wa kotun cewa bai samu damar ganawa da mai gidansa ba kan batun da aka gabatar masa a Abuja, lamarin da ya sa ya nemi kotun ta ɗage sauraron ƙarar domin ba shi damar sanar da gwamnan da lauyoyinsa halin da ake ciki.
Mai Shari’a Ado Muktar da ke hukunci kan al’amarin, ya amince kuma ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 15 ga Disamba. Zainab, ‘ya ce a wajen tsohon gwamnan Jihar Kano kuma abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Da yake zantawa da manema labarai bayan zaman kotun, Bature ya ce ya samu labarin shigar da gwamnan ƙara ne ta rahotannin da suka karaɗe kafafen labarai kan batun, don haka ya karɓi bayanan kotu a madadin gwamnan amma bai kai ga sanar da shi halin da ake ciki ba, yana mai kira ga ‘yan jarida da su kula da yadda suke ruwaito labarai kan al’amarin musamman ganin yadda ya shafi cikin gida.
