Kotu ta hukunta jami’in tsaron filin jirgin saman Kano kan yunƙurin fasa-ƙwaurin gwal-gwalan biliyan N4.4

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano ta ƙaddamar da hukunci akan wani Ali Baffa bisa laifin yunƙurin fasa-ƙwaurin ɗanyen gwal mai nauyin kilogram 22.2, wanda adadin kuɗinsa ya kai Naira biliyan 4.4. Mai Shari’a, Sale Shuaibu, ya umarci a ƙwace gwal-gwalan a damƙa wa Gwamnatin Tarayya biyo bayan yanke wa Baffa hukunci.

A wata sanarwa da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta fitar a ranar Talata, ta tabbatar da hukuncin da kuma ƙwace gwal ɗin. Ta ce an kama Baffa ne a ranar 11 ga Yuni, 2026 a filin jiragen sama na Mallam Aminu Kano da ke Kano.

EFCC ta bayyana cewa, Baffa, wanda Sufeto na 1 ne na jami’an tsaron filin jiragen (AVSEC), an zargi shi ne da ɓoye ƙananan akwatinan gwal-gwalan a cikin wandunansa domin kauce wa binciken jami’an tsaro kafin ya miƙa su ga fasinjojin da ke tafiya ƙasar waje domin shigar da su ta ɓarauniyar hanya.

Hukumar ta bayyana cewa, Sashenta na kula da lamuran badaƙalar filaye da kadarori ne ya gudanar da atisayen kamen bayan umarnin Shugaban EFCCn ga dukkan cibiyoyi na su yi hoɓɓasa wajen daƙile ayyukan fasa-ƙwaurin albarkatun ƙasa da maƙudan tsabar kuɗaɗe ta filayen jiragen sama na ƙasa-da-ƙasa. Bayan faɗaɗa bincike, an kuma cafke ƙarin wasu mutum biyu, Aushabu Nasidi da Mukhtar Muhammad Ɗan Zaria kan zargin su da hannu a lamarin. EFCC ta zargi Nasidi da kai wa Baffa ƙunshin gwal-gwalan, yayin Ɗan Zaria ya kai wa Nasidi.

Hukumar ta ce, an samu Nasidi da tsabar kuɗaɗen ƙasashen waje masu yawa. Daga cikinsu akwai Riyal ɗin Saudiyya 3,000, Iira ɗin Turkiyya 40,000, Danarin Kuwait 199.75, Fesos ɗin Philippines 20,700, Dalar Australiya 80, 310, Renminbin Chana 4,000, Dinarin Aljeriya 40,000, Dalar Hong Kong 40, Forints ɗin Hungary 26,000 da kuma 1,000 na Dinarin Sudan.

Ɗan Zaria ya shaida wa masu bincike cewa ya yi fasa-ƙwaurin jimillar kilogram 40.2 na gwal tsakanin ranar 1 zuwa 11 ga Yuni, 2026 ta amfani da irin salon. A sanarwar da EFCCn ta fitar a ranar 11 ga Yuni, ta ce za a maka mutane ukun a kotu da zarar an kammala bincike akansu.

By Babaji

Leave a Reply