
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, ta ce ta yi nasarar kama wasu mutane guda huɗu, ciki har da wata mata bisa zargin su da hannu a sacewa da halaka wani yaro ɗan shekara 14 a shirin tabbatar da cewa ɗanta ya gaji dukiyar mahaifinsu shi kaɗai. Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun yi zargin cewa mutanen sun kitsa makircin kashe yaron, mai suna Mahmoud Auwal tare da wasu yara uku na mijinta domin bai wa yaronta shi kaɗai damar gaje dukiyar gidan.
Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an samu rahoton ɓatar marigayin ne a ranar 29 fa Afrilun 2026, lamarin da ya sa tawagar daƙile ayyukan garkuwa ta rundunar ta hanzarta ƙaddamar da bincike domin gano haƙiƙanin al’amari.
A cewarsa, an kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi mai suna Muhammad Musa Isma’il, ɗan shekara 20 a ranar 3 ga Nuwamba, wanda ya amsa cewa sun ɗana wa yaron tarko ne shi da wani Abubakar Muhammad Isa mai shekara 27 da Auwal Muhammad mai shekara 26 yayin cimma manufar tasu. Matasan sun amsa cewa sun kitsa makircin halaka yaron da kuma jefar da gawarsa, wadda daga bisani jami’an ‘yan sanda suka gano.
Da aka faɗaɗa bincike, an yi nasarar kama wadda ake zargi da jagorantar kitsa shirin mai suna Hajiya Ruƙayya Auwal mai shekara 20, wadda abokiyar zaman mahaifiyar marigayin ne a wajen mijinsu. Rundunar ta kuma yi zargin cewa, matar ta ɗauko hayar wasu ‘yan daba da nufin su farmaki ɗaya daga cikin wanda ake zargin don kada ya fallasa ɗanyen aikin nasu.
Tuni dai ‘yan sandan suka ce za a miƙa su ga kotu da zarar an kammala bincike akansu. Kwamishinan rundunar, Ibrahim Bakori Adamu, ya yi tir da al’amarin tare da tabbatar wa iyalan marigayin cewa za a yi musu adalci a kai.
