Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Wani jigo na jam’iyyar NDC a Jihar Zamfara, Mohammed Sani Takori Gummi ya zargi shugabancin jamiyyar ta ƙasa da rashin cancanta, son kai, nuna banbancin addini, mulkin ƙabilanci, mamayar yanki, da almubazzaranci da kuɗi a matsayin abinda yake kawo tarnaƙi ga jam’iyyar.
Takori, a cikin wata sanarwa kan halin da jam’iyyar ke ciki, ya ce jam’iyyar da waɗanda suka kafa ta suka yi wahala suka gina ta da ƙarfin su, dukiyarsu, jajircewarsu da sadaukarwa, a yau an ƙwace ta hannun wasu bisa nuna ƙarfi da ba su da alaƙa da ainihin manufarta.
Takori ya ce a yau, NDC ta gudanar da wasu shirye-shiryenta, tare da halartar shugaban jam’iyya, ɗan takarar shugaban ƙasa da mataimakinsa.
Ya ce, haka nan akwai mambobin kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da kwamitin aiki na ƙasa (NWC), tare da wasu mutane da dama waɗanda matsayinsu da ayyukansu a cikin jam’iyya ba su da tabbas.
“Taron da aka gudanar, babu wani abu mai ma’ana da aka tattauna game da ainihin alƙibla, ƙalubale da makomar jam’iyyar,” in ji Takori.
Ya koka da cewa wasu mutane uku ne kawai suke juya akalar harkokin jam’iyyar, kuma abin baƙin ciki, dukkansu daga yanki ɗaya ne.
Takori ya bayyana kansa a matsayin misali a cikin wannan mummunan hali da jam’iyyar ke ciki.
“Na zuba Naira miliyan 7.5 da na samu da wahala a cikin aikin kare jam’iyyar kuma na yi rajistar mambobi 35,000 ga jam’iyyar. A yau, an watsar da ni gaba ɗaya”. Inji Takori
Ya bayyana cewa da farko ya yanke shawarar kada ya halarci taron, amma ɗansa, Usman, ya matsa masa, kuma daga ƙarshe ya girmama gayyatar.
Takori ya ce jam’iyyar da suka kafa da hangen nesa, da jajircewa mai yawa a cikinta, a yau ta zama wacce son kai na addini, muradun yanki da ƙaruwar saɓani a tsakanin manyan ‘yan siyasa suka mamaye.
“Tafiya zuwa inda muke nufi ta zama mara tabbas, cin hanci da rashawa da maye gurbin ‘yan takarar da aka kayar da mutane da muke da shakku kan matsayin siyasa sun zama abin da ake yi kullum a NDC,” in ji shi.
Ya zargi shugaban jam’iyyar da miƙa dukkan ikonsa ga wasu mutane kaɗan waɗanda ba su da fahimta kaɗan ko basu san yadda aka kafa jam’iyyar ba.
“Ba na jin tsoron kowa, kuma waɗanda ke da alhakin hakan su gode wa Allah cewa ba a ba ni damar yin magana a yau ba,” in ji Takori
Ya ce fatan samun nasarar jam’iyyar, ko da a kudu, yana ƙara zama mara tabbas, balle a Arewa, inda shugaban jam’iyyar yake ƙoƙarin sayar da makomar siyasar jam’iyyar.
Game da shari’ar da jam’iyyar ta shiga, Takori ya ce daga kotun farko har zuwa matakin da take a yanzu, babu tabbacin ina aka dosa.
Ya ce su huɗu waɗanda suka ɗaukaka ƙara a cikin shari’ar an watsar da su gaba ɗaya. An gaya musu cewa an ba wa lauyoyi aikin wakilcin su kuma an shigar da takardun da suka dace.
“Abin baƙin ciki, babu ɗaya daga cikinmu da ya san lauyoyin da ke wakilcinmu. Haka nan an hana mu sanin abin da ke cikin takardun da ranakun da aka tsara na zaman kotu,” in ji shi.
A lokacin ƙaddamar da jam’iyyar, ya ce, lokacin da Ma’aji ya gabatar da bayanin kashe kudaden da aka yi, ya fashe da dariya kan adadin da aka ce an kashe a kan shari’a. Wannan, in ji shi, ya tayar da manyan tambayoyi game da gaskiya, lissafi da sarrafa dukiyar jam’iyyar.
Takori ya gargaɗi cewa jam’iyyar na iya fuskantar ficewar wasu daga cikin waɗanda suka kafa ta a cikin kwanaki masu zuwa.
“Har yanzu, mutane biyu masu muhimmanci waɗanda muka yi aiki tare don kafa jam’iyyar sun janye. Wasu da dama suna tunanin yin hakan,” in ji shi.
Ya bayyana cewa ƙungiyar ‘yan Arewa ta jam’iyyar za ta haɗu nan ba da jimawa ba ta yi taron manema labarai.
